UNICEF za ta agazawa Najeriya a harkar ilmi da kiwon lafiya

UNICEF za ta agazawa Najeriya a harkar ilmi da kiwon lafiya

Mun samu labari cewa Kungiyar nan ta UNICEF ta majalisar dinnkin Duniya mai gidauniyar tallafawa kananan yara ta yi alkawarin cigaba da taimakawa Najeriya kamar yadda ta saba.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wannan kungiya za ta cigaba da yin abin ta ke yi wajen ba Najeriya gudumuwa a harkar ilmin boko da kiwon lafiya da kuma tsare-tsaren tsabtace tsabtace.

Majalisar dinkin Duniyar ta yi alwashin wannan ne ta hannun UNICEF wanda ke da alhakin taimakawa yara. Wani babban jami’in kungiyar UNICEF ta Duniya ya shaidawa Najeriya wannan.

A lokacin da Maulid Warfa ya ziyarci jihar Katsina, ya bada tabbacin cewa UNICEF na da shirin cigaba da kokarin da ta ke yi tare da hada kai da gwamnoni wajen samun cigaba a Najeriya.

KU KARANTA: An cafke masu satar kananan yara a cikin Jihar Kaduna

Mista Maulid Warfa wanda ya ke kula da jihohin Kano da Katsina da Jigawa ya bada wannan alwashi ne a Ranar 26 ga Watan Satumba sa’ilin da ya gana da gwamnatin Aminu Bello Masari.

Warfa ya yabawa kokarin da Aminu Masari ya ke yi wajen inganta harkar ilmi a Katsina. A na sa bangaren, mai girma gwamnan ya nuna godiya kan irin ayyukan da ita ma kungiyar ta ke yi.

UNICEF ta shigo da wani tsari na SHAWN wanda ya kunshi ayyukan inganta tsabta da lafiya da kuma ruwan sha a Katsina. Gwamnan ya ce zai bada duk wani goyon baya da ake bukata.

Har ila yau gwamnan ya bayyana rashin ilmin addini da na Boko a yankin Dajin Rugu a matsayin abin da ya sa Makiyaya su ke ta’adi a jihar Katsina inda yake sa rai UNICEF ta bada taimakon ta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel