2027: PDP Ta Canza Dan Takarar Gwamna a Kano, Ta Jawo Dan Tsohon Shugaban Najeriya
- PDP tabbatar da Muhammad Sani Abacha, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha, a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2027
- An gudanar da sabon zaɓen fidda gwani ne bayan tsohon ɗan takarar jam’iyyar, Muhammad Bello Dalha, ya janye
- Jam’iyyar PDP ta kuma sasanta ɓangarorin da ke rikici, inda Yusuf Ado Kibiya ya zama abokin takarar Abacha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano ta tabbatar da Muhammad Sani Abacha a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Wannan sanarwa ta biyo bayan janyewar Muhammad Bello Dalha, wanda a baya ya samu tikitin jam’iyyar PDP bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa an cimma matsayar ne ranar Laraba yayin wani taron Kwamitin Zartarwan PDP na Jihar Kano, inda aka gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani domin maye gurbin Dalha.

Kara karanta wannan
Kwankwaso da Obi sun zo da wani tsari da zai iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027
PDP ta tsaida Muhamman Abacha takara
Shugaban PDP na Jihar Kano, Dr Bello Gambo Bichi, ya ce Dalha, wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar a baya, ya janye da kansa bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki a Kano da Abuja.
A cewarsa, janyewar ta tilasta gudanar da sabon zaɓe bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe da suka dace.
“A baya mun gudanar da zaɓen fidda gwani inda aka bayyana Muhammad Bello Dalha a matsayin wanda ya yi nasara, amma bayan shawarwari tsakanin masu ruwa da tsaki a Kano da Abuja, ɗan takarar ya yanke shawarar janyewa.
“Doka ta ce idan ɗan takara ya janye, dole ne a gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani domin maye gurbinsa. Wannan ne ya kawo mu nan yau,” in ji Bichi.
Abdullahi ya ce an gudanar da aikin ne bisa ƙa’idojin PDP da dokokin zaɓe da suka dace, yana mai cewa Abacha ya cika dukkan sharuddan tsayawa takara.
PDP ta sasanta ɓangarorinta a Kano
Jam’iyyar ta kuma sanar da cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin ɓangarorin da ke takaddama a cikinta, inda Bichi ya ce an bai wa ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki, kujerar mataimakin gwamna.
Saboda haka, an naɗa Yusuf Ado Kibiya, tsohon shugaban wani ɓangare na PDP kuma tsohon Kwamishinan Filaye da Noma, a matsayin abokin takarar Abacha.

Source: Facebook
Bichi ya ce an cimma matsayar ne bayan gudanar da shawarwari masu yawa da kuma ƙoƙarin sasanta ɓangarorin jam’iyyar, kamar yadda The Cable ta rahoto.
“Bayan shawarwari masu yawa da sulhu, mun amince mu bai wa ɓangaren Turaki kujerar mataimakin gwamna a nan Kano. Da wannan, babu sauran ɓangare-ɓangare a PDP ta Kano. Mun sasanta,” in ji shi.
PDP ta rungumi hadakar yan adawa
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta amince da shirin G-100 na hada jam’iyyun adawa domin samar da tsayayyen dan takara.
Ta bayyana cewa hadin kan ‘yan adawa zai taimaka wajen kwace mulki daga APC da sake gina Najeriya tare da magance talauci, rashin tsaro.
Asali: Legit.ng
