Tubabban 'yan bindiga a Katsina sun sanar da Masari su waye ke haddasa rikici a Katsina

Tubabban 'yan bindiga a Katsina sun sanar da Masari su waye ke haddasa rikici a Katsina

A ranar Laraba ne tubabbun 'yan bindiga a Katsina suka sanar da gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, cewa wasu daga cikin jami'an rundunar 'yan sanda da dakarun sojin Najeriya ne ke rura wutar aiyukan ta'addanci a jihar domin kawai su samu kudi.

Sun yi gargadin cewa matukar jami'an tsaron basu daina karbar kudi da shanu a hannunsu ba, ba za a samu wani canji ta fuskar samun zaman lafiya ba a jihar.

Kungiyoyin 'yan bindigar sun bayyana hakan ne ranar Laraba yayin wata tattunawa da gwamna Masari a wani zaman sulhu da aka fara yi a makarantar Firamare ta Gbagegi dake Dankolo a yankin karamar hukumar Dandume.

Tubabbun 'yan bindigar da suka gana da gwamnan sun fito ne daga kananan hukumomin Dandume da Sabuwa - kananan hukumomin da hare-haren 'yan bindigar suka fi tsananta.

Yawaitar hare-haren 'yan bindiga, satar shanu da garkuwa da mutane ne suka tilasta gwamna Masari yanke shawarar yin sulhu da 'yan ta'addar domin samun zaman lafiya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindigar Katsina: Su waye su?

Shugaban kungiyar 'yan bindigar jihar Katsina, Idris Yayande, ya fada wa gwamna Masari cewa hallayyar jami'an tsaro na karbar kudi daga hannusu ne yasa duk kokarin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ki yin wani tasiri.

"Sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sune ke rura wutar garkuwa da mutane da sauran aiyukan ta'addanci da ake yi a jihar Katsina ta hanyar bamu hadin kai domin mu basu kudi. Ba zamu iya yarda da su ba gaskiya, gara mu yi aiki da 'Yansakai," a cewar Yayande.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar 'Yansakai, Lawal Tosho, ya nuna amincewarsa da jawabin Yayande tare da zargin Sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da wasu 'yan siyasar jihar da hannu wajen ganin cewa shirin sulhun da gwamnan ya fara bai yi tasiri ba. Tosho ya yi ikirarin cewa: "ina da dukkan hujjojin da zan iya kare abinda na fada".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel