Yanzu Yanzu: Yan bautar kasa 2 sun mutu a wani mummunan hatsari a Katsina

Yanzu Yanzu: Yan bautar kasa 2 sun mutu a wani mummunan hatsari a Katsina

Wasu yan bautar kasa biyu a jihar Katsina, a ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta sun mutu a wani mummunan hatsarin mota, da ya afku a kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Kankara da ke jihar.

Yan bautar kasar sun kasance mace guda daga jihar Akwa Ibom da kuma wani namiji daga jihar Anambra.

Zuwa yanzu dai hukumar kula da NYSC a Katsina bata fitar da cikakken bayani akansu ba.

Wasu shiadu sun bayyana cewa yan bautar kasar na kan tafiya ne tare da abokan aikinsu cikin wata mota dauke da rubutun ‘Corpers for Christ’ domin halartan wani biki a wani cocin Katolika da ke Funtua lokacin da hartsarin ya afku.

Motar na dauke da lamba MAN 45 AA.

Gwamna Aminu Masari, wanda ke a hanyarsa ta zuwa Danja a lokacin da riski hatsarin, yayi umurnin cewa ayi amfani da motarsa wajen kwasan gawawwakin yan bautar kasar da takwarorinsu zuwa Katsina.

Gwamnan na a hanyarsa ta zuwa Danja domin halartan ta’aziyyar Alhaji Saleh Danja wanda ya mutu sanadiyar hatsarin mota a ranar Asabar a Tsanni da ke karamar hukumar Batagarawa da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya yi Allah wadai da harin da matasa suka kai wa Ekweremadu

Marigayi Alhaji Danja, ya kasance makusancin Gwamna Masari.

Wani dan bautar kasa ya shaida wa gwamnan cewa ruwan sama mai karfi da aka yi ne ya sanya hanyar yin tsantsi, sannan cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da direban yayi kokarin sa birki.

Yace ruwan da ke a kan hanyar ya sa motar yin tsalle sannan ya daki wata bishiya da ke kusa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng