Matsalar tsaro: Masari zai shiga cikin daji don tattaunawa da yan bindiga
Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya umarci sakataren gwamnatin jahar Katsina, Mustapha Inuwa ya shirya zaman tattaunawa tsakanin gwamnati, shuwagabannin hukumomin tsaro da yan bindiga domin tattauna batun sulhu.
Rahoton kamfanin dillancin labaru ya bayyana cewar gwamnan ya umarci sakataren gwamnatin ya shirya wannan tattaunawa ne a sansanin yan bindigan dake cikin daji, kamar yadda daraktan watsa labaru na fadar gwamnatin jahar, Abdu Labaran ya tabbatar.
KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Sojoji sun kai ma Boko Haram harin kwantan bauna, sun kashe 2
Labaran ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, inda yace gwamnan ya dauki wannan mataki ne a karshen wani taron masu ruwa da tsaki a kan tsaro daya gudana a ranar Laraba.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai mataimakin gwamna, Mannir Yakubu, kaakakin majalisar jahar, Tasiu Musa Maigari, sakataren gwamnatin jahar Mustapha Inuwa, Sarkin Katsina, shuwagabannin kananan hukumomi, da kuma wakilan Fulani makiyaya.
“Na kira taron ne don baiwa masu ruwa da tsaki daman bayar da gudunmuwarsu wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a jahar, kuma kashe kashen da ake yi a Katsina ya isa haka, dole ne a kawo karshensa ba tare da bata lokaci ba.
“A shirye nake na tattauna dasu a duk inda suke domin yin sulhu, tare da kawo karshen ayyukan yan bindiga a jahar Katsina, koda wannan mataki bai haifar da dai mai ido ba, za mu shawo kan matsalar nan ta wata hanyar.” In ji shi.
A wani labarin kuma, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya gayyaci shuwagabannin al’ummar Fulani dake zaune a kananan hukumomi guda 9 na jahar Katsina domin tattauna hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a jahar.
Gwamnan ya yi wannan zaman tattaunawa da Fulani ne sakatariyar gwamnatin jahar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta inda aka yi zube ban kwaryata tsakanin bangarorin biyu da nufin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a jahar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng