Buhari ya yabawa kwazon da gwamna Masari yake yi a jihar Katsina

Buhari ya yabawa kwazon da gwamna Masari yake yi a jihar Katsina

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana farin ciki a kan kyakkyawar kulawa da kuma ci gaba na aminci da al'ummar jihar Katsina ke samu tsawon shekaru hudu a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya yi godiya kwarai dangane da yadda gwamna Masari ya yi tsayuwar daka wajen tabbatar da ci gaban al'ummar jihar Katsina wadda ta kasance mahaifarsa.

Furucin shugaban kasar na bayyana abinda ke cikin zuciyarsa ya zo ne a ranar Alhamis yayin kaddamar da gyaran babbar hanyar da ta ratsa cikin garuruwan Fago, Katsayal, Kwasarawa, Jirdede, da kuma Koza.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, babbar hanyar mai tsayin mita dubu 38 wadda ta ratsa cikin kananan hukumomi hudu na jihar Katsina, an fara gininta na farko a yayin da shugaba Buhari ke jagorancin hukumar Petroleum Trust Fund PTF da aka kafa da rarar kudin man fetur.

A cewar hadimin shugaban kasar, Buhari ya kuma kaddamar da wata sabuwar hanya mai tsayin mita dubu 16 wadda ta karade garuruwan Kwanar Sabke, Kokutu, Makangara, Haukan Zama, Nareje, Madoma, Nasarawa, Magamiyo, Dan'Aunai, Kwanar Dila, Gurje, Magale, Sabon Garin Kogon, Burtu, Dado, Minawa, Subashi, Dutsawa, Nafasa da kuma Dutsi.

KARANTA KUMA: Nadin Ministoci: Buhari ya sabawa kundin tsarin mulki kasa - Lauya

Shugaban kasar ya ce hanyoyin za su taimaka kwarai dagaske wajen bai wa manoma damar fidda amfanin gonakinsu zuwa kasuwanni cikin sauki, da kuma bai wa al'ummar gari dama ta zirga-zirga zuwa makarantu da cibiyoyin neman lafiya ba tare da wata tangarda ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel