Babban Sarki a Najeriya Ya Fito Ya Nuna Goyon Baya ga Tinubu

Babban Sarki a Najeriya Ya Fito Ya Nuna Goyon Baya ga Tinubu

:

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya buƙaci ƴan Najeriya da su goyi bayan ɗorewar shugabanci maimakon neman sauyi kawai
  • Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da Darakta Janar na yakin neman zaben APC, Abdulaziz Yari, ya kai masa ziyara a fadarsa
  • Yari ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a fannin tattalin arziki gami da dakatar da hauhawar farashi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benin – Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya buƙaci al'ummar ƴan Najeriya da su goyi bayan ɗorewar shugabancin Bola Tinubu a maimakon neman sauyin mulki a 2027.

Oba ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na APC (PCC), Abdulaziz Yari, ya ziyarce shi.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa Arewa ba za ta juyawa Tinubu baya ba a 2027

Sarkin Benin da Abdulaziz Yari
Sarkin Benin tare da Sanata Abdulaziz Yari a Edo. Hoto: Abdulaziz Yari
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Sanata Yari ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa fadar Benin domin neman albarka da addu'o'in goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.

Oba Ewuare II ya jaddada cewa fadar mulkin Benin ba ta siyasa ba ce, don haka kada a fassara maganarsa a matsayin goyon bayan wata jam'iyya.

Ya rubuta cewa:
"Masarautar Benin ba 'yar siyasa ba ce. Babu amfanin neman sauyi. Wannan ba yana nufin ina ɓangaren wata jam'iyya ba ne. Shin akwai wanda yake kamili kamar yadda nake magana yanzu? Babu kowa. Ina son zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Kiran sarkin ga shugabanni

Sarkin ya kuma yi kira ga tsofaffin gwamnoni, sanatoci da sauran shugabannin siyasa da su haɗa kai waje guda domin ci gaban ƙasa, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jam'iyya mai mulki da ta adawa.

A nasa ɓangaren, Abdulaziz Yari ya bayyana cewa makasudin ziyarar shi ne neman albarkar sarki ga Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

An fara rade radin kulla sabuwar hadaka domin kifar da Tinubu a 2027

Yari ya ƙara da cewa:

"Haɓakar tattalin arzikin Najeriya (GDP) ya tashi daga kashi 2.7 a shekarar 2023 zuwa kashi 3.9, yayin da hauhawar farashi ya ragu daga kashi 22.9 zuwa kashi 15.9, sannan gwamnati ta daidaita kasuwar canjin kudi."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mataimakin Gwamnan jihar Edo, Rt. Hon. Dennis Idahosa, wanda ya wakilci Gwamna Monday Okpebholo, ya godewa sarki bisa albarkar da ya sa wa tafiyar, inda ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya dace ya yi wa'adi na biyu.

Rikicin Wike da 'yan APC

A wani labarin daban, kun ji cewa karuwar adawa tsakanin ƴan siyasa gabanin zaɓen 2027 ta haifar da tsami tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da gwamnonin jam'iyyar APC.

Nyesom Wike, wanda ke hidima a gwamnatin APC mai ci, yana ƙoƙarin ƙulla wata haɗaka mai suna 'Rainbow Coalition' a jihar Rivers domin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Sai dai a daren ranar Litinin, Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya martana a fakaice cewa gwamnonin ba za su goyi bayan kowani nau'in ƙawance ko haɗaka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng