Mutanen Yankin Daura su na neman kujerar Gwamnan Katsina

Mutanen Yankin Daura su na neman kujerar Gwamnan Katsina

A halin yanzu an fara kira ga mulki ya koma yankin Daura a jihar Katsina ganin cewa mutanen Birni da bangaren Karaduwa watau Yankin Funtuwa sun samu damar yin gwamna a jihar Katsina.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da wani dogon rahoto, mutanen Daura su na ganin lokacinsu ya yi ne bayan ganin cewa tun daga 1999 zuwa yanzu, ‘yan siyasan Birnin ne ke yin mulki a Katsina.

Umaru Yaradua da Ibrahim Shehu Shema wanda su ka yi mulki na shekaru 16 sun fito ne daga tsakiyar Jihar. Sai a 2015 ne Karaduwa su ka samu na su ya samu gwamna kan Aminu Masari.

Shi kan shi Alhaji Saidu Barda wanda ya fara mulki a jihar Katsina a karkashin jam’iyyar NRC ya fito ne daga cikin Katsina ta tsakiya. Wannan ya sa sauran jama’a ke gani ba a yi da su a jihar.

Haka zalika sauran wadanda su kayi mulki a Katsina lokacin ta na cikin tsohuwar jihar Kaduna watau Lawal Kaita da Abba Musa Rimi duk babu ainihin ‘Dan yankin Daura da kewayen Funtua.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta yi babban yunkurin karbe Jihar Kogi daga hannun APC

A 2023, Daurawa su na so su taki irin sa’ar da Funtua ta samu a 2015 inda Aminu Masari ya samu zama gwamna a karon farko daga yankin, duk da irin tarin al’ummar da su ke da shi a shiyyar.

Daga cikin abin da ya sa mutanen yankin Daura su ka kara huro wuta a 2023 shi ne ganin cewa su na da rikakkun ‘yan siyasa yanzu a kasa, sannan kuma yankin na da kananan hukumomi har 11.

Daga cikin wadanda ake tunanin za su nemi takara daga yankin na Daura a 2023 akwai Ahmed Dangiwa, da kuma tsohon Sanata Hadi Sirika wanda Ministan jirage ne tun a gwamnatin Buhari.

Sauran ‘yan siyasan gida da za su iya neman kujerar gwamna a 2023 sun hada da shugaban NRC, Ibrahim Alasan, da Ahmad Babba-Kaita da El-Marzuq Ahmed da kuma Umar Gwajo Gwajo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng