An Fitar da Hasashen Makomar Tinubu, Atiku da Obi a Zaben 2027

An Fitar da Hasashen Makomar Tinubu, Atiku da Obi a Zaben 2027

  • Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Afegbua ya ce tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai zo na biyu, yayin da Peter Obi zai zo na uku a zaɓen
  • Kwamishinan ya bayyana cewa tseren zaɓen 2027 zai fi karkata ne tsakanin Tinubu, Atiku da Obi, yayin da ya yi watsi da damar sauran ’yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi hasashen sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu zai zo na farko.

Rahotanni sun nuna cewa Afegbua ya ce Atiku Abubakar zai zo na biyu, yayin da Peter Obi zai zo na uku a fafatawar da za a yi.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa Arewa ba za ta juyawa Tinubu baya ba a 2027

Peter Obi Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Manyan 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya. Hoto: Peter Obi|Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Twitter

Afegbua ya ware Tinubu, Atiku da Obi

Jaridar Punch ta wallafa cewa Afegbua ya yi wannan hasashen ne yayin da yake nazarin damar manyan ’yan takarar adawa a wata hira.

Ya ce fafatawar da za a yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance ne tsakanin Tinubu, Atiku da Obi.

Kwamishinan ya ce:

“Zaɓen tseren mutum uku ne, don Allah kada ku dame ni da batun Seyi Makinde da ba shi da muhimmanci.”

Ya yi watsi da damar Makinde

Afegbua ya kuma yi tambaya kan damar Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda ke neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APM.

Ya ce bai ga irin tasirin APM a Najeriya da zai sa a ɗauki Makinde a matsayin ɗan takarar da zai iya yin tasiri a zaɓen ba.

Afegbua ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa Makinde ke nuna ƙwarin gwiwa wajen neman shugabancin ƙasar.

Afegbua ya yi watsi da Sowore

Kara karanta wannan

Duk da yana shugaban al'umma, babban sarki ya goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027

Kwamishinan ya kuma yi watsi da damar ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC, Omoyele Sowore, da sauran ’yan takarar adawa.

Omoyele Sowore a wani waje a Abuja
Dan takarar shugaban kasa na AAC. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Ya bayyana wasu daga cikin ’yan takarar da cewa masu tayar da hankali ne kawai, yana mai cewa ba su cikin manyan waɗanda zai iya yin mamaki a zaɓen.

The Sun ta rahoto cewa Afegbua ya ce:

“Atiku Abubakar zai zo na biyu. Peter Obi zai zo na uku. Shugaba Bola Tinubu zai zo na farko.”

Kwamishinan ya ce hasashensa ya samo asali ne daga ƙididdiga, bincike da kuma nazarin yadda jam’iyyar APC take da ƙarfinta da kuma raunin da take da shi a zaɓe.

Atiku ya soki Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan farashin man fetur da ya ce ya kai N1,470 kan kowace lita.

Atiku ya bayyana cewa ’yan Najeriya na biyan wannan farashin ne duk da cewa danyen mai a yanzu yana kan $102.52 kan kowace ganga, wanda ya yi ƙasa da $147 da ya kai a 2008.

Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin bayyana yadda ake tafiyar da wasu kudin gwamnati, musamman kudin Asusun Tarayya (FAAC) da kuma kudin da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng