Harkar noma: Sabuwar shinkafa ta fara shigowa Jihar Katsina

Harkar noma: Sabuwar shinkafa ta fara shigowa Jihar Katsina

Kusan mako guda kenan a kasuwannin jihar Katsina, duk inda ka je maganar shinkafa ake yi bayan Manoma sun fara samun amfanin gona. Wannan ya sa farashin shinkafan ya fara sauka.

Rashin darajar da masara ta yi a bara ya sa Manoma da-dama a bana sun komawa shinkafa. Sai dai a halin yanzu, wadanda su ka cire shinkafan su na fuskantar karancin masu ciniki a kasuwanni.

Tsadar kudin taki yana cikin dalilan da su ka sa Manoma su ka rabu da masara su ka kama shinkafa a wannan shekarar kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana a wani rahoto da ta fitar a Litinin.

Wani babban Manomi a Kudancin jihar Katsina yace su na sa rai bana za su samu amfani sosai na shinkafa ganin irin ruwan sama da aka samu. Manoman su na kuma ganin cewa za su samu riba.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta zama Hedikwatar masu garkuwa da mutane a Najeriya

Haka wani babban Manomin shinkafa a Dandume ya ce ba a samun masu sayen hatsi a kasuwa ne yanzu saboda ba a dade da fara cire amfani ba, ya ce za su jira kafin su fara saida kayan gona.

Manomin ya nuna cewa za su dakata har hatsi su sha iska tukuna kafin su kai su kasuwa. Sai bayan shinkafa ta bushe ne kamfanoni ke neman ta, ya ce yanzu ba a fara ciniki ba tukun.

A bara war haka, farashin buhu ya kai N8000 har zuwa N10000. Wannan karo, abin da ake saida buhun shinkafar bai wuce N8000 inda a wasu wurare ma kudin buhun ya sauko har zuwa N5000.

Shinkafar da ake kira Farar Jar Naira ce mai tsada a kasuwa. Ana saida ta ne a kan N8000 duk buhu. Ana saida buhun irin Jeap a N6000. Sauran shinkafan ba su haura N5000 a halin yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel