An Fara Guna Guni bayan Rashin Sanin inda Shugaban INEC Ya Shiga

An Fara Guna Guni bayan Rashin Sanin inda Shugaban INEC Ya Shiga

  • Obidient Movement ta nemi INEC ta bayyana inda Shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, yake bayan Rhoda Gumus ta bayyana a matsayin shugabar riƙon kwarya
  • Ƙungiyar ta ce babu sanarwar hukuma da ta bayyana lokacin ko dalilin da ya sa Amupitan ya miƙa ragamar hukumar ga Gumus
  • Ta kuma nemi INEC ta bayyana ko Amupitan ya fita daga ƙasar da kuma irin ayyukan hukuma da ya gudanar yayin da ba ya hedikwatar hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Obidient Movement ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi bayani kan inda shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, yake da kuma ayyukan da yake gudanarwa.

Ƙungiyar ta yi wannan buƙatar ne bayan Kwamishiniyar INEC ta Ƙasa, Farfesa Rhoda Gumus, ta bayyana a matsayin shugabar riƙon kwarya yayin wani taro da tawagar Tarayyar Afirka (AU) a Abuja.

Kara karanta wannan

Sanata Yari na jagorantar kamfen din Tinubu, ya yi babban rashi a rayuwa

An nemi Amupitan an rasa
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Gumus ta karɓi tawagar AU

A ranar Talata, 15 ga Satumba, INEC ta wallafa wani saƙo a shafinta na X, inda ta bayyana Gumus a matsayin shugabar riƙon kwarya ta hukumar.

Gumus ce ta karɓi Tawagar Bincike da Tantance Buƙatun Zaɓe ta Tarayyar Afirka, wadda ta ziyarci hedikwatar INEC da ke Abuja.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Harkokin Wajen Habasha, Demeke Mekonnen, ta je Najeriya ne domin tantance shirye-shiryen ƙasar na babban zaɓen 2027.

Gumus na cikin kwamishinonin INEC na kasa, kuma sunanta yana cikin jerin kwamishinonin da aka wallafa a shafin hukumar.

Obidient Movement ta nemi bayani

A cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar na kasa, Dr Yunusa Tanko, ya sanya wa hannu a shafin X, ƙungiyar ta ce bayyanar Gumus a matsayin shugabar riƙon kwarya ta haifar da tambayoyi kan inda Amupitan yake.

Tanko ya ce, a saninsu, babu wata sanarwa daga INEC da ta bayyana cewa Amupitan ya miƙa aikinsa ga wani mutum, ko a matsayin riƙon kwarya ko na dindindin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ya yi murabus

“A wajen Obidient Movement da ’yan Najeriya, babu wata sanarwar da ta bayyana cewa Farfesa Amupitan ya miƙa ragamar aikinsa ga wani, ko a matsayin riƙon kwarya ko na dindindin,” in ji shi.

Ya ce hakan ya haifar da tambayoyi kan inda shugaban hukumar yake a yanzu, jadawalin ayyukansa da kuma dalilin rashin kasancewarsa a hedikwatar INEC.

An nemi INEC ta bayyana tafiyarsa

Ƙungiyar ta nemi INEC ta bayyana inda Amupitan yake, lokacin da ya bar Abuja da kuma dalilin da ya sa ya yi hakan.

Ta kuma nemi hukumar ta bayyana wanda ya ba da izinin tafiyar, da kuma ko shugaban ya fita daga ƙasar.

Idan ya fita daga Najeriya, ƙungiyar ta ce INEC ya kamata ta bayyana irin ayyukan da ya gudanar a wajen ƙasar.

Ta tambayi ko ya gana da Tinubu

Obidient Movement ta kuma nemi INEC ta bayyana ko Amupitan ya gana ko kuma yana da shirin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma, ta nemi bayani kan ko shugaban hukumar ya gana ko yake shirin ganawa da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ko kuma wani wakilin jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Daga fara kamfen, manyan magoya bayan Tinubu suna rikici a tsakaninsu

Ƙungiyar ta ce irin waɗannan bayanai na da muhimmanci domin a fahimci yanayin ayyukan hukumar da kuma dalilin da ya sa Kwamishina Gumus ke gudanar da ayyukan shugaban INEC a halin yanzu.

Ana neman sanin inda Amupitan yake
Farfesa Joash Amupitan na gabatar da jawabi Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

ADC ta aika sako ga INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta mika bukatar ta ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Jam'iyyar ADC ta bukaci hukumar INEC ta hana malaman jami’a da aka san suna da alaƙar siyasa zama jami’an tattara da haɗa sakamakon zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng