Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari
Wasu Sanatoci 2 da Gwamna 1 sun fara harin ajiye siyasa. Ike Ekweremadu, Danjuma Goje, da Rt. Hon. Amin Masari za su ajiye kambu na siyasa a 2023 a Najeriya.
Hotunan wasu yara sun fara yawaita a kafofin sada zamuntar zamani bayan da suka gina azuzuwan karatunsu da kasa. Jaridar rariya ce ta fara wallafa hotunan tare da bayyana yadda yaran suka gina azuzuwan karatu da kasa...
Ana neman sake bude wata Jami’a a jihar Shugaban kasa ta Katsina. Sanata Bello Mandiya watau Sanatan na Kudancin jihar Katsina ya kawo maganar.
Gwamnatin Jihar Katsina ta na daf da tace Malaman da za su rika wa’azi. Wata jaridar kasar nan ta kawo mana wannan rahoto a cikin farkon makon nan.
Gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kashe akalla naira miliyan 52,901,098.74 wajen gyaran babban masallacin juma’a na Usman Danfodio dake unguwar Modoji a cikin garin Katsina.
Sakamakon zaben da aka bayyana a kananan hukumomin Kogi ya nuna Gwamna Yahaya Bello mai neman tazarce ya yi wa PDP da SDP raga-raga a Mahaifarsa.
Daga karshe bayan daukan dogon lokaci ana shirye shirye, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya aika ma majalisar dokokin jahar Katsina jerin sunayen sabbin kwamishinoninsa.
Labarin Katsinawa da Zamfarawan nan har su 30 da aka kai wata kasar Afrika zuwa aikin bauta na wata 3 zai sa saka kuka. Yanzu dai sun fito sun bada labarin duk yadda ta kaya da su.
Darajar Shugaban kasa ta sa ana yin wasu aikace-aikace a Daura. Daga cikin hanyoyin da aka gama akwai titin da ya tashi tun daga Fago-Katsayal-Kwarasawa Jirdere-Koza to Kawanar Sabke da Sandamu-Baure.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari
Samu kari