Sanatoci sun yi na’am da kawo Jami’ar koyon aikin noma a Funtua

Sanatoci sun yi na’am da kawo Jami’ar koyon aikin noma a Funtua

Majalisar dattawan Najeriya sun amince a kirkiro jami’ar koyon aikin gona a Garin Funtua da ke jihar Katsina. Sanatan yankin Kudancin Katsina, Bello Mandiya ya kawo kudirin a majalisa.

Za a aika wannan kudiri na Sanata Bello Mandiya zuwa gaban majalisar wakilai domin a samu magana daya. Idan an ci nasara za a aikawa shugaban kasa wannan kudiri domin ya sa hannu.

A cikin makon nan ne wannan bukata ta Sanatan APC, Bello Mandiya, ta tsallake mataki na biyu a majalisar dattawan. ‘Dan majalisar ya na ganin cewa kawo jami’a a yankin zai taimaka kwarai.

A na sa hangen, Mandiya ya nuna cewa kafa jami’a ta musamman domin koyon aikin gona zai bunkasa harkar noma a kasar tare da cin ma nasarar fadada tattalin arzikin Najeriya daga mai.

KU KARANTA: Wani 'Dan Majalisar Jihar Imo ya riga mu gidan gaskiya

Jami’ar za ta rika koyar da kwas na fasaha da bincike a harkar noma wanda su ke da tasiri ga cigaban da kasar ta ke buri. A halin yanzu gwamnatin Najeriya ta bada himma kan harkar noma.

“Muradun kafa jami’ar da sauran cibiyoyin bincike da koyon karatu shi ne fadada ilmin harkar noma da fasaha ga kowa ba tare da la’akari da jinsi, kabila, launi ko akidar siyasa ba.” Inji sa.

Haka zalika Sanatan na Kudancin Katsina ya bayyana cewa: “Makarantar za ta samar da nagartaccen horaswan kimiyya wanda tubali ne na ilmin fasaha da kuma cigaban aikin gona.”

‘Dan majalisar ya na da ra’ayin cewa kafa jami’a a Yankin zai kara dankon zumunci da hadin kai a Najeriya. Kwanakin baya dai aka kafa tubalin gina wata jami’a ta sufuri a Garin Daura a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng