APC da Gwamna Yahaya Bello sun yi wa PDP dukan babban bargo a Okene

APC da Gwamna Yahaya Bello sun yi wa PDP dukan babban bargo a Okene

Mun samu labari cewa sakamakon zaben gwamna a jihar Kogi inda abin ya kaure tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP mai hamayya bai yi wa Musa Wada na PDP kyau ba.

Mai girma gwamna Yahaya Bello ya lallasa Injiniya Musa Wada na PDP da kuma ‘yar takarar jam’iyyar SDP, Natasha Akpoti a karamar hukumar Okene da ke cikin yankin Kogi ta tsakiya.

Gwamnan ya tashi da kuri’u 112,764 a Garin Okene yayin da jam’iyyar PDP da SDP su ka iya tashi da kuri’u 139 da kuma 50 kacal. APC ta ba PDP mai bin ta a baya kuri’u 112, 625 a wannan Gari.

INEC ta sanar da wannan sakamako da bakin Olanrewaju Samuel wanda ya yi aikin a karamar hukumar. Natasha Akpoti wanda ta fito daga wannan yanki ta soki yadda aka gudanar da zaben.

Dama can kun ji labari cewa APC ta samu kuri’a 716 ne a akwatin rumfar zaben gwamnan. Manyan ‘yan takarar jam’iyyar hamayya; Musa Wada da Natasha Akpoti ba su samu ko kuri’a ba.

KU KARANTA: 'Yan daba sun yi barna a rumfar Sanata Dino Melaye

Gwamna Yahaya Bello ya kada kuri’arsa ne a Mazabar Okene-Eba/Agassa/Ahache a akwati na 11 da ke cikin karamar hukumar Okene. Wannan gagarumar nasara za ta taimakawa jam’iyyar APC.

Yahaya Bello mai neman tazarce ya tserewa sauran ‘yan takara a sauran shiyyoyin da mutanen Ebira su ka fi karfi. Gwamnan ya fito daga kabilar Ebira ne wanda ba su saba mulkin jihar ba.

An yi tunanin cewa Natasha Akpoti wanda ta fito daga shiyya guda da gwamnan za ta kawo masa cikas. Sai dai yanzu sakamakon zabe sun nuna cewa jam’iyyar SDP ba ta tabuka abin kirki ba.

Haka zalika ‘dan takarar mataimakin gwamna na APC, Edward Onoja, ya doke jam’iyyun PDP da SDP a akwatinsa da ke Emoyokwu a Garin Ogugu da ke cikin karamar hukumar Olamaboro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel