Sokoto: Sunayen Malamai da Za Su Tantance Kalaman Sheikh Musa Lukuwa kan Annabi SAW
- Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya kafa kwamitin mutum 14 domin bincike kan kalaman da aka yi kan iyayen Annabi Muhammad SAW
- Kwamitin zai binciki batutuwan da Sheikh Musa Lukuwa ya gabatar da kuma tasirinsu ta fuskar Shari’a da addini
- Kwamitin ya kunshi manyan malamai, masana shari’a, jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyi da darikun Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kafa kwamiti mai mutum 14 domin binciken kan kalaman da wasu malaman musulunci suka yi da wasu ke ganin batanci ne ga Annabi SAW.
Mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa, ne ya bayyana kafa kwamitin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Source: Twitter
Premium Times ta ce kwamitin da Yahaya Boyi ke jagoranta zai duba tasirin batutuwan da Sheikh Musa Lukuwa ya gabatar ta fuskar doka da addini, wadanda ake zargin sun yi rashin mutunci ga akidar wasu.
An kafa kwamitin ne sakamakon damuwa da aka nuna kan wasu kalamai da aka yi a bainar jama’a wadanda suka kara ta’azzara zaman dar-dar na addini a fadin jihar.
Daya daga cikin kalaman da suka tunzura jama'a akwai batun makomar iyayen Annabi Muhammad SAW, wadanda wasu suka nuna bacin ransu.
Abin da kwamitin zai bincika
Daga cikin abubuwan da aka dora wa kwamitin akwai yin nazari mai zurfi kan matsayin Shari’a game da batutuwan da Sheikh Lukuwa ya gabatar tare da bai wa gwamnatin jihar shawarar matakin da ya dace ta dauka.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnatin jihar Sokoto cikin kwanaki 14.
Kwamitin ya kunshi manyan malamai, masana harkokin shari’a, manyan jami’an gwamnati da wakilan manyan kungiyoyi da darikun Musulunci daga ciki da wajen jihar ta Sokoto da ke Arewa maso Yamma.
Sunayen mambobin kwamitin
Malaman da gwamnatin Sakkwato ta zakulo ta sanya a cikin wannan kwamiti sun hada da:

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka
Yahaya na Malam Boyi (Sarkin Malamai) – Shugaba
Muhammad Isah Mafara – Mamba
Bello na Malam Boyi – Mamba
Mansur Ibrahim, mni – Mamba
Mansur Ibrahim Sa’id – Mamba
Wakilin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatas Sunnah (Izala) ta Kaduna – Mamba
Wakilin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatas Sunnah (Izala) ta Jos – Mamba
Wakilin Kungiyar Darikar Tijjaniyyah – Mamba
Wakilin Kungiyar Darikar Qadiriyyah – Mamba
Wakilin Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) – Mamba
Wakilin Majalisar Masarautar Sarkin Musulmi ta Sokoto – Mamba
Kwamishinan Addini na jihar Sakkwato – Mamba
Lawal Maidoki – Mamba
Barr. Gandi Umar Muhammad, mni – Sakatare

Source: Facebook
An rufe masallacin Sheikh Musa Lukuwa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke Mabera bayan harin da ya yi sanadin kisa.
Gwamnati ta bayyana masallacin a matsayin wurin da aka aikata laifi zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an ba da wani sabon umarni.
Ta kuma nisanta kanta daga duk wani mutum, ba tare da la’akari da matsayinsa ba, da ke fakewa da addini domin zagon kasa ko nuna rashin girmamawa ga Annabi Muhammad (SAW), iyayensa, iyalansa da sahabbansa.
Asali: Legit.ng

