Buhari da Osinbajo su wallafa duk dukiyoyin da su ka mallaka – SERAP
An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakinsa watau Farfesa Yemi Osinbajo, su bayyanawa Duniya dukiyoyinsu.
Kungiyar SERAP mai zaman kan-ta, ta aikawa fadar shugaban kasa wasika, ta na nema a wallafa abin da takardun CCB na shugabannin su ka kunsa.
Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 5 ga Watan Junairu, 2019, SERAP ta kuma hada gwamnonin Najeriya 36 a cikin wannan wasika.
SERAP ta hannun mataimakin Darektanta, ta nemi shugabannin kasar Najeriyar su wallafa kadarorin da su ka mallaka domin Duniya ta gani.
A jawabin da Kolawole Oluwadare ya fitar, ya bayyana cewa sun aikawa shugabannin takardun FOI ne kamar yadda dokar tsarin mulki ta tanada.
KU KARANTA: Buhari ya maidawa Bakare martani, ya ce jama'a za su zabi Magajinsa a 2023
Mataimakin Darektan na SERAP ya nuna cewa dokar FoI ta bada damar tilastawa shugabannin su fadi dukiyar da su ke da ita saboda bin diddiki.
A cewar SERAP, alkawarin da shugaba Buhari ya yi wa jama’a na cewa zai fadawa Duniya abin da ya mallaka, ya sa ta aiko masa wannan takarda.
Oluwadare ya nemi shugaban kasar ya bukaci mukarrabansa su bi sahu, su bayyana abin da su ka tara a Duniya, mako daya da samun takardar nan.
“Dukiyar da mu ke bukatar a bayyana sun hada da: Kudin da aka ajiye a banki, da gine-gine, da hannun jari a kamfanoni da wasu kasuwancinsu.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng