Katsina: Gwamnati za ta tace Malaman da za su rika wa’azi – Hafiz Mika’il

Katsina: Gwamnati za ta tace Malaman da za su rika wa’azi – Hafiz Mika’il

Jaridar The Sun ta ce Hukumar shari’ar ta jihar Katsina, ta shirya domin fara tantance Malamai masu gudanar da wa’azi a masallatai, da bainar jama’a da kuma sauran wurare a fadin jihar.

Shugaban wannan hukuma ta harkar shari’a da aka kafa a jihar, Al-Hafiz Mika’il, ya bayyana wannan kamar yadda jaridar kasar ta kawo rahoto a Ranar Litinin, 2 ga Watan Disamban 2019.

Shugaban Alkalin shari’a na jihar Katsina, Al-Hafiz Mika’il ya ce za a tantance Malaman jihar ne domin tabbatar da cewa masu yin wa’azi su na bin dokokin da addinin musulunci ya tanada.

Alkalin Alkalan kotun shari’ar ya ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron karawa juna sani. An gudanar da wannan taro ne musamman ga manyan jami’ai da kuma Alkalan kotun shari’a.

KU KARANTA: Yadda na zama Maraya ina da 'Dan karamin Yaro - Buhari

Har ila yau, babban Mai shari’a Al-Hafiz Mika’il, ya kuma yabawa gwamnatin jihar Katsina mai-ci a game da matakin da ta dauka na dabbaka shari’a ga Musulman da ke zaune a cikin jihar.

Shugaban Alkalan jihar Katsina baki-daya, Mai shari’a Musa Danladi, ya halarci taron. A jawabinsa, ya koka a game da karancin Alkalai da ake fama da su da za su rika sauraron shari’a.

Mai shari’a Danladi ya bada shawara ga mutanen Gari da su rika kawo kara gaban kuliya, a maimakon daukar mataki a hannunsu. Bayan nan kuma ya ja-kunnen Alkalai da su yi gaskiya.

Babban Lauyan gwamnatin Katsina, Ahmad El-Marzuq, ya wakilci Mai girma gwamna Aminu Bello Masari a wajen taron. Gwamnan ya yi kira ga Alkalai su yi aikinsu ba tare da tsoro ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel