Ma’aikatan jihar Katsina za su fara cin moriyar sabon karancin albashi daga Janairun 2020

Ma’aikatan jihar Katsina za su fara cin moriyar sabon karancin albashi daga Janairun 2020

Rahotanni sun kawo cewa ma’aikatan jihar Katsina za su fara cin moriyar sabon karancin albashi daga watan Janairun wannan shekara ta 2020.

Shugaban kwamitin jihar kan sabon karancin albashi kuma babban sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Mustapha Inuwa ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu yayinda yake jawabi ga manema labarai a gidan Janar Muhammadu Buhari, Katsina kan matsayar da aka kai tsakanin gwamnatin jihar da kuma kungiyar kwadago na jihar.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Kwamrad Hussaini Hamisu a jawabinsa ya yi godiya ga tawagar gwamnati kan yadda suka zama masu gaskiya a yayin tattaunawar wanda a cewarsa ya sawwaka aikinsu.

Dukkanin bangarorin biyu sun sanya hannu a yarjejeniyar tare da gyare-gyare a albashin ma’aikatan.

KU KARANTA KUMA: Manyan ayyuka 12 da gwamnatin Buhari za ta kammala a 2020 – Shugaban kasa ya tabbatar

A wani jawabi makamancin haka, mun ji cewa Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da biyan ma'aikata a jihar karancin albashi na N30,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga Mohammed Baba, sakataren gwamnatin jihar zuwa ga manema labarai a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, a Bauchi.

A cewar jawabin, sabon umurnin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, daga ranar 1 ga watan Janairu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng