Daga karshe Gwamna Masari ya fidda sunayen sabbin kwamishinoninsa kamar haka
Daga karshe bayan daukan dogon lokaci ana shirye shirye, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya aika ma majalisar dokokin jahar Katsina jerin sunayen sabbin kwamishinoninsa.
Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya mika sunayen mutanen da yake muradin nadawa a majalisar zartarwar gwamnatin jahar Katsina ga majalisar dokokin jahar ne domin tantancesu kamar yadda doka ta shimfida.
KU KARANTA: Ajali ya yi kira: Ruwan kududdufi ya cinye wani mutumi dan shekara 40 a jahar Kano
Wadannan sabbin kwamishinoni sun hada da:
1- Hon Musa Adamu
2- Rt Hon Yau Umar Gwajogwajo
3- Hon Tasiu Dandagoro
4- Hon Abdullahi Imam
5- Hon Dr Rabe Nasir
6- Hon Faruk Jobe
7- Hon Muktar Gidado
8- Hon Sani Aliu Danlami
9- Prof Badamasi Charanchi
10- Hon Abdulkadir Zakkah
11- Tpl Usman Nadada
12- Haj Rabiya Mohd
13- Alh Kasim Umar Mutallab Funtua
14- Alh Abdulkarim Yahaya
15- Hon Mustapha Mahmud Kanti
16- Hon Yakubu Nuhu Danja
17- Hon Hamza Suleman Faskari
Daga karshe majalisar dokokin jahar Katsina ta yanke shawarar fara tantance sabbin kwamishinonin daga ranar Litinin mai zuwa, inda suka zasu tantancesu a rukuni 3, a ranakun Litinin, Talata da Laraba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng