Gaskiyar abun da ya sa yan bindiga suka kai hari da kashe sama da mutane 30 a kauyukan Katsina - Masari

Gaskiyar abun da ya sa yan bindiga suka kai hari da kashe sama da mutane 30 a kauyukan Katsina - Masari

Gwamna Aminu Bello Masari a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu, ya yi bayani kan abun da ya haddasa hare-hare da kisan sama da mutane 30 da yan bindiga suka yi a yammacin ranar Juma’a a kauyukan Tsayau da Dankar da ke karamar hukumar Batsari na jahar Katsina.

Mummunan harin da yan bindiga kimanin dozin daya suka kai ya yi sanadiyar rasa rayuka musamman Ma dattawa sannan suka kona gidaje da dama yayinda yan ta’addan suka sace kayayyaki na miliyoyin naira.

Sai dai gwamnan ya ce rahoton tsaro da ke wajensa ya nuna cewa kisan wasu makiyaya biyu a yankunan ne ya haifar da ramuwar gayya wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka, baya ga sace-sace da kuma raunata wasu da dama da maharan suka yi.

Masari wanda ya yi Allah wadai da harin da ya bayyana a matsayin mafi muni a watanni bakwai da suka gabata ya fayyace lamarin ne a yankin Malumfashi a lokacin raba kayayyakin tallafi da Sanata mai wakiltan Katsina ta Kudu a majalisar dattawa, Bello Mandiya ya yi.

Gaskiyar abun da ya sa yan bindiga suka kai hari da kashe sama da mutane 30 a kauyukan Katsina - Masari
Gaskiyar abun da ya sa yan bindiga suka kai hari da kashe sama da mutane 30 a kauyukan Katsina - Masari
Asali: UGC

Ya kuma gargadi mazauna yankuna a kan kai wa makiyaya hari domin guje ma sake afkuwar mummunan lamari a Batsari.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda suka amfana daga shirin da su yi amfani da abun da suka samu.

Ya nuna yakinin cewa hakan zai kawo ci gaba ga rayuwar wadanda suka amfana da shirin.

Da yake magana, Shugaban Majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ba mutanen jahar tabbacin cewa majalisar dokokin tarayyar za ta cigaba da ba shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya wajen kawo karshen ta’addanci a jahar da kasar baki daya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta yi umurnin kama tsohon Shugaban Kwastam, Dikko

Da ya ke jaje ga mutanen kan rashin da suka yi, Lawan ya bayyana Katsina a matsayin gidansa na biyu bayan Yobe.

Ya alakanta son da yake yiwa jahar a kan dadewar da suka yi da Buhari, Masari da sauran manyan yan siyasar jahar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng