APC: Jam’iyyar mu ta na nan ko Shugaban kasa Buhari ya tafi Inji Badaru

APC: Jam’iyyar mu ta na nan ko Shugaban kasa Buhari ya tafi Inji Badaru

Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki, sun fito su na cewa jam’iyyarsu za ta kasance ta na nan daram-dam a kasa har bayan tafiyar Muhammadu Buhari.

A cewar gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa, alkawarin da jam’iyyar APC ta yi na kawo cigaba a Najeriya, shi ne zai cigaba da ceton jam’iyyar har nan gaba.

Mai girma gwamnan na APC ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin da ‘Yan jarida su ka jefa masa a hedikwatar jam’iyyar da ke babban birnin tarayya.

Rahotanni sun ce a karshen makon nan ne gwamnonin jam’iyyar APC da ke lemar kungiyarsu ta PGF, su ka yi wani taro a karkashin shugabansu, Simon Lalong na jihar Filato.

Kungiyar gwamnonin APC sun maida martani ne game da kalaman da gwamna Kayode Fayemi ya yi a kan cewa akwai yiwuwar APC ta watse idan Buhari ya gama mulkinsa.

KU KARANTA: Masu hangen 2023 su yi hakuri tukuna a gyara kasa yanzu - Buhari

APC: Jam’iyyar mu ta na nan ko Shugaban kasa Buhari ya tafi Inji Badaru
Gwamna Badaru ba ya ganin rushewar Jam'iyyar APC nan kusa
Asali: Twitter

“Abin da zan iya cewa a kan jam’iyya shi ne shi ne shugabannin jam’iyya da kungiyar gwamnoni su na kokari dare da rana domin a shawo kan matsalolin da ake fuskanta.”

“Kuma ina tabbatar da cewa Mai girma shugaban kasa kansa ya na duba lamarin domin tabbatar da cewa an magance rikicin shugabancin” Inji gwamnan na jihar Jigawa.

Gwamnan ya kare bayani a kan rikicin da cewa: “Za a shawo kan rikici cikin ‘dan kankanin lokaci. Mu na aiki a kan wannan, kuma da yardar Ubangiji, zai zama tarihi.”

“A game da wargajewar APC bayan shugaba Buhari, shugaban kasa ya yi alwashin cigaba da mara mana baya domin jam’iyyar APC ta dore har ta kara karfi bayan ya tafi.”

Gwamna Fayemi ya ce idan ba su yi hankali ba, abin da ya hada kan APC – wanda shi ne Buhari, ya na tafiya, za a samu matsala muddin ba a kawo tsare-tsare da ka’idoji ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel