Ana Wata ga Wata: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Cire Wani Tallafi a 2027

Ana Wata ga Wata: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Cire Wani Tallafi a 2027

  • Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta kawo ƙarshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga 2027
  • Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce za a cire tallafin a hankali tare da biyan tsoffin basussukan ɓangaren wutar lantarki
  • Ya ce babu shirin ƙara kuɗin wutar lantarki nan take yayin da gwamnati ke shirin kawo ƙarshen tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kawo ƙarshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga 2027 domin samar da tsarin da zai dawwama a ɓangaren wutar lantarki.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana hakan yayin wata ganawar manema labarai ta baya-bayan nan.

Tegbe.
Ministan harkokin wutar lantarki na Najeriya, Joseph Tegbe Hoto: Joseph Tegbe
Source: Instagram

Tribune Nigeria ta rahoto cewa ministan ya yi magana kan yawan basussukan da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki da kuma shirin gwamnati na hana ƙaruwar basussuka.

Kara karanta wannan

Iran: An samu shaidun da ke nuna Trump ya aikata babban laifi a duniya

Yadda aka tsara cire tallafin lantarki

Tegbe ya ce gwamnati za ta cire tallafin a hankali yayin da take aiki wajen biyan tsoffin basussukan ɓangaren.

“Mun samu umarnin Shugaban Ƙasa na biyan tsofaffin basussuka da kuma samar da tsare-tsare masu ɗorewa domin tabbatar da cewa ba a ƙara tara wasu basussuka ba,” in ji Tegbe.

Ministan ya ce shirin cire tallafin ba yana nufin yan Najeriya za su rasa fa’idodin da suke samu a yanzu ba, yana mai tabbatar cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta samar da wutar lantarki.

“Na yi muku alkawari, shekara mai zuwa, da yardar Allah, za mu kawo ƙarshen wannan abin da ake kira tallafi a ɓangaren wutar lantarki.
"Shugaban Ƙasa ba zai hana Najeriya wani abu ba. Za mu tabbatar da cewa masu amfani da wutar lantarki a Najeriya sun ci gaba da samun wuta tare da inganta ayyukan wutar lantarki,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ce wutar lantarki ta inganta a Najeriya, ana masa godiya

Shin za a kara kudin wuta a Najeriya?

Tegbe ya kuma ce babu wani shirin gaggawa na ƙara kuɗin wutar lantarki yayin da gwamnati ke shirin kawo ƙarshen tallafin.

Ministan ya bayyana cewa an samu ci gaba wajen samar da wutar lantarki, inda wasu wuraren da a baya suke fama da dogon lokaci ba tare da wuta ba yanzu suke samun wutar lantarki har na tsawon sa’o’i 18 a rana.

Lantarki.
Turakon da ke dakon wayoyin raba wutar lantarki a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Facebook
“Wuraren da ba su da wuta kwata-kwata tsawon watanni uku yanzu suna samun wuta na tsawon sa’o’i 18. Wasu wurare sun kira ni suka ce, ka rage gudu, komai da ke cikin firijinsu yana daskarewa," in ji shi.

Tegbe ya tuna cewa a lokacin tantance shi da Majalisar Dattawa, ya yi alkawarin cewa ’yan Najeriya za su fara ganin sauyi a samar da wutar lantarki cikin watanni uku zuwa shida.

Ministan Tinubu ya cika baki kan lantarki

Kun ji cewa Joseph Tegbe, ya bayyana cewa yadda mutane ke samun wutar lantarki ba katsewa ya sa wasu ƴan ƙasa roƙonsa ya rage ƙarfin wutar da ake kawowa.

Ministan ya amince da ƙalubalen da ke gaban ɓangaren, inda ya bayyana cewa yawancin kayayyakin lantarki a ƙasar sun wuce shekaru 40.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262