Babbar Magana: An Kai Korafin Dan Majalisa gaban NDLEA kan Zargin Shan Hodar Iblis
- Wasu mutanen mazabar Kaduna North sun roƙi NDLEA ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin amfani da hodar iblis da ake yi wa ɗan majalisarsu
- Korafin na su ya biyo bayan zargin da kanin dan majalisar ya fito ya yi a kafafen sada zumunta ranar 29 ga Agusta 2026, amma ba a tabbatar da shi ba
- Masu ƙorafin sun ce ba sa neman a ɗauki dan majalisar a matsayin mai laifi, sai dai hukumar ta tantance ko akwai dalilin doka na fara bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Wasu daga cikin mutanen mazabar tarayya ta Kaduna North sun kai ƙara ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), kan dan majalisarsu.
Masj korafin sun nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kan wani zargin amfani da hodar iblia da ya shafi ɗan majalisar wakilai, Hon. Mohammed Bello El-Rufai.

Kara karanta wannan
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce an sanya wa takardar ƙorafin kwanan wata 8 ga Satumba, 2026, kuma Abubakar Hayatu na gundumar Kabala da Musa Tukur na Unguwar Gaji ne suka sanya hannu a madadin sauran mutanen.
Zargin ya fito daga dan’uwansa
Masu ƙorafin sun ce sun ɗauki matakin ne bayan Bashir El-Rufai, ɗan’uwan Bello na jini, ya yi wasu zarge-zarge a kafafen sada zumunta ranar 29 ga Agusta.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai da dama sun ruwaito musayar kalaman da ta gudana a kafafen sada zumunta, amma sun kuma bayyana cewa ba a samu tabbaci mai zaman kansa kan zargin ba.
A takardar da suka aika wa shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), masu ƙorafin sun jaddada cewa ba sa neman hukumar ta ɗauki Bello a matsayin mai laifi.
Sun kuma ce ba sa neman a tilasta masa yin wani gwajin da bai dace da doka ba, sai dai su na son hukumar ta tantance lamarin domin gano ko akwai dalilin doka na gudanar da bincike.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu
Meyasa suka gabatar da korafin?
A cewar masu korafin, zargin da Bashir El-Rufai ya yi ya haɗa da batun amfani da hodar iblis, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Sun ce an ruwaito zargin a kafafen yaɗa labarai da dama tare da yaɗa shi sosai a intanet, don haka suka miƙa wa NDLEA bayanan da suke da su domin hukumar ta yi nazari da kanta.
Sun bayyana cewa ba sa gabatar da zargin a matsayin tabbatacciyar hujja ba.
Sun kuma ce kasancewar Bashir ɗan’uwan Bello na jini na iya zama dalilin da ya sa zargin ya jawo hankali, amma dangantakar iyali ko rikicin da ke tsakaninsu ba ya tabbatar ko karyata zargin.
Sun ce batun ya shafi jama’a
Masu ƙorafin sun ce zargin amfani da hodar iblis da ya shafi ɗan majalisar tarayya da ke kan mukami bai kamata a rufe shi kawai da cewa rikicin iyali ne ba.
A cewarsu, idan hujjoji masu inganci suka tabbatar da cewa an aikata laifin amfani da miyagun ƙwayoyi, lamarin na iya shiga ƙarƙashin dokokin Najeriya na yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
Abin da suka nema daga NDLEA
Masu ƙorafin sun yi nuni da Sashe na 3 da na 4 na dokar NDLEA, inda suka ce dokar ta ɗora wa hukumar alhakin aiwatar da dokokin da suka shafi miyagun ƙwayoyi da gudanar da bincike.
Sun roƙi NDLEA ta karɓi bayanan, ta tantance su da kanta, sannan ta duba ko akwai dalilin doka na fara bincike.
Sun kuma nemi hukumar ta ɗauki duk wani matakin bincike da doka ta ba ta dama idan ta gano akwai isasshen dalili, tare da sanar da su matsayar da ta ɗauka kan ƙorafin idan hakan zai yiwu.

Source: Original
Matashi ya kashe jami'in NDLEA
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami’in hukumar NDLEA da ke jihar Bauchi ya rasa ransa bayan wani mutum da ba a san ko wanene ba ya caka masa wuka.
Rundunar NDLEA ta Bauchi ta ayyana wanda ake zargin da aikata kisan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng