Wata Sabuwa: Trump bai Gama da Iran ba, Ya Yi Barazana ga Tarayyar Turai
- Donald Trump da ke shugabantar Amurka ya yi barazanar kakaba wa Tarayyar Turai haraji mai tsanani ko dakatar da cinikayya
- Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta gabatar da shirin bai wa Kanada damar zama mamba 'yar kungiyar EU
- Kanada na ƙara ƙulla dangantaka da EU yayin da take fuskantar takaddamar cinikayya da barazanar haraji daga gwamnatin Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage cinikayya da Tarayyar Turai ko kuma kakaba mata haraji mai tsanani.
Trump ya yi barazanar ne bayan Tarayyar Turai ta gabatar da shirin bai wa Kanada damar zama mamba 'yar kungiyar.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026 yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan shirin EU, cewar rahoton tashar Aljazeera.
Trump ya ce shirin na iya zama “abin dariya”
Trump ya bayyana shirin a matsayin abin da yake ganin ba shi da ma’ana, yana mai cewa zai ɗauki matakin da ya dace idan ya ɗauki shirin a matsayin wani hari ga Amurka.
“Ina ganin abin dariya ne,” in ji Trump lokacin da aka tambaye shi game da shirin.
Ya ce idan matakin ya kasance abin da Amurka za ta ɗauka a matsayin “aikin ƙiyayya”, zai iya kakaba wa ƙasashen Turai haraji mai tsanani ko kuma dakatar da cinikayya da su kan wasu kayayyaki.
Trump ya ƙara da cewa idan manufar shirin ta kasance mai kyau, ba zai damu ba, amma idan ya gano cewa manufar ba ta da kyau, zai iya kakaba wa Turai haraji mai matuƙar tsanani.
EU na son ƙara kusantar Kanada
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta gabatar da shirin ne gabanin jawabin da Firaministan Kanada, Mark Carney, zai yi a Majalisar Tarayyar Turai.
Von der Leyen ta nemi ƙara haɗin gwiwa tsakanin EU da Kanada a fannonin fasaha, tsaro da makamashi.
Carney ne shugaban gwamnati na farko daga wajen Turai da ya halarci jawabin shekara-shekara na EU mai taken “State of the European Union”.
Da take jawabi a Majalisar Tarayyar Turai da ke Strasbourg, von der Leyen ta ce ya kamata Brussels da Ottawa su ƙara kusantar juna yayin da tsarin dokokin ƙasa da ƙasa ke fuskantar barazana.
Kanada na neman ƙarfafa alaƙa da EU
Carney ya kasance yana neman ƙara ƙarfafa dangantaka da EU yayin da Kanada ke ƙara shiga cikin takaddamar cinikayya da Amurka.
Ana sa ran zai yi jawabi a Majalisar Tarayyar Turai ranar Alhamis, yayin da ziyararsa ke da nufin ƙarfafa shirye-shiryen taron EU da Kanada da za a gudanar a Montreal a wata mai zuwa.
Von der Leyen ta ce lokaci ya yi da EU da Kanada za su wuce haɗin gwiwar da ya ta’allaka kawai kan cinikayya zuwa wani faɗaɗɗen “ƙawancen makoma”.

Source: Getty Images
Amurka za ta sayar da makamai ga Israila
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta shirya sayar da makamai masu yawa ga babbar kawarta Israila.
Gwamnatin ta Trump n kan hanyar amincewa da wani kunshin makamai da darajarsa ta kai dala biliyan 2.8 da za a sayar wa Isra’ila.
Asali: Legit.ng


