Ana kai wasu manyan ayyuka Daura saboda Shugaba Buhari

Ana kai wasu manyan ayyuka Daura saboda Shugaba Buhari

A halin yanzu an kammala ayyuka da dama a Garin Daura da ke jihar Katsina, yayin da ake kan cigaba da wasu, har kuma ake shirin cigaba da kawo wasu duk a Mahaifar shugaban Najeriya.

Wani binciken Daily Trust ya nuna cewa kayan aiki sun cika Garin Daura inda ake gina makarantu, tituna, hanyoyin ruwa da sauransu, hakan na nufin Yankin na cin arzikin shugaban kasa Buhari.

Rahoto ya nuna cewa da wuya a samu wata ma’aikatar tarayya da ba ta wani sabon aiki ko aka farfado da wani aikin da aka ajiye ko ake fadada wasu kwangiloli a cikin Mahaifar shugaban kasar.

Bayan kwangilolin da ma’ikatun wutar lantarki, ayyuka, gidaje, kiwon lafiya da ilmi su ke yi, wasu Abokan siyasar shugaban kasar da na-kusa da shi, su kan yi na su 'dan kokarin a cikin Garin Daura.

Akwai tituna da hanyoyin ruwa da ake yi na kusan kilomita 40 wanda ‘yan kwangila 4 su na tsakiyar aiki. Za kuma a fara wani sabon titi mai cin kusan kilomita 90 wanda zai yi wa Daura zobe.

Bayan wannan, a wa’adin farko na shugaban kasa Muhammadu Buhari an zuba hanyoyin titi da na ruwa a Garin na Daura. An kuma gina makarantu na masu fama da nakasa duk a wannan tsohon Gari.

Ana sa ran nan gaba kadan za a soma aikin ginin jami’ar sufuri a Daura. Tuni an warewa wannan makaranta da za a gina eka 6000 na fili. Za kuma a fara aikin ginin makarantar koyon aiki a Garin.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Katsina yasamu yabo daga Kungiyar UNICEF

Akwai ayyukan da an kammala yanzu haka, wannan sun hada da asibitin sojin saman Najeriya da aka yi da kuma cibiyar koyon sana’o’i na NDE wanda yanzu ta yaye dalibai bayan an kashe miliyoyi.

Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari ta gina sashen mata masu haihuwa a babban asibitin gwamnati na Daura. Gwamnatin tarayya ta tado da batun aikin Sabke Dam wanda zai ba Garin ruwa.

Ban da wadannan aikace-aikace, an gina makarantu da dama da kuma layin wutar lantarki. Nan gaba kuma za a fara maganar aikin dogon jirgin kasa da wani dakin karatu na zamani da aikin ruwan sha.

An kuma shara titi daga Fago zuwa Katsayal har kwanar sabke. Bayan nan kuma an yi titi wanda ya tashi daga Garin Sandamu zuwa Baure. Gwamnan Katsina ya kuma gyare otel din gwamnati da ke Garin.

Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya na kashe kudi wajen gyara babban masallacin Garin. Aliko Dangote zai batar da Naira miliyan 100 domin ganin an sabunta wannan babban masallaci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel