Burkina Faso: Labarin yadda aka yaudare mu aka saida mu cikin bauta

Burkina Faso: Labarin yadda aka yaudare mu aka saida mu cikin bauta

Daily Trust ta kawo wani rahoto game da wasu mutanen Najeriya da aka yaudara har aka jefa su cikin bauta a kasar Burkina Faso inda su ka bayyana yadda su ka samu kansu a matsayin Bayi.

Usman Suleiman ya na cikin mutane 30 da aka ce za a ba aiki a Sokoto, kafin ya ce mene, sai ya iske kansa a Garin Gaoua wanda ke kusa da babban birnin Burkina Faso watau Ouagadougou.

“Kamar dai asiri aka yi mana.Babu wanda ya iya magana ko yace wani abu. Mu dai kurum bin umarni mu ka yi ta yi, tun daga nan Katsina, zuwa Legas har Benin, daga nan zuwa Garin Gaoua.”

“Da farko fada mana aka yi cewa a Sokoto za mu yi wani aiki, amma sai mu ka ga mun buga wani wurin dabam, kuma dai mu ka gaza magana da mu ka ga abin da ke faruwa.” Inji Suleiman.

“A waje mu ke barci, mu roki abincin da za mu ci. Wasu su ka kwanta rashin lafiya babu magani.” Sulaimen mai maata uku yace sun ci bakar wahala na watanni uku ba tare da damar dawowa ba.

Shi kuma Audu Sa’ad yace a lokacin da aka isa da su wannan Gari, sai aka ba su kayan hake-hake domin a birne wasu igiyoyin sadarwa. Sa’ad yace aikin na bogi domin bugewa su ka yi dangatali.

KU KARANTA: An sace wasu Makiyaya 6 a Arewa maso Gabashin Najeriya

Sa’ad yake cewa bayan sun fahimci cewa babu wani aikin da za su yi, sai su ka fara huro wutan za su dawo gida. A nan fe aka bayyana masu cewa akwai kudi a wuyannsu, domin cinikinsu aka yi.

Wannan Bawan Allah yake cewa daga nan su ka koma kwana a masallaci su na yawon neman abin da za su ci. Abin dai har ya kai jami’ai su ka damke su da laifin su na yin bara a cikin Garin.

Sani Adamu yake cewa: “Na lura akwai matsala tun bayan makonni hudu da zuwan mu Garin bayan hana mu komawa hutun sallah a gida kamar yadda aka yi mana alkawari da can a baya.”

Matsalar rashin fahimtar harshe ya kara jagwagwala zaman na mu. Babu wanda za mu iya yi wa bayani. Ba mu da kudi, babu abinci, babu damar mu kuma yi magana da Iyali.” Inji Adamu.

Abdullahi Amin shi ma ya bada labarin yadda su ka gamu da haza kafin Jakadiyar Najeriya a kasar ta Burkina Faso, Hajiya Rahmatu Ahmed, ta sa baki har ta tuntubi gwamnatin jihar Katsina.

Wani Mai safarar mutane mai suna Alhaji Usman Wagini shi ne aka zargi ya saida wadannan mutane ga wata mata a kasar Benin. An ceto wadannan mutane kuma an cafke wannan Mata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel