Zaben 2023: Ekweremadu, Goje, da Gwamna Masari za su ajiye kambu

Zaben 2023: Ekweremadu, Goje, da Gwamna Masari za su ajiye kambu

Mun tattaro maku jerin wasu gawurtattun ‘Yan siyasan Najeriya da su ke shirin rabuwa da takara daga zabe mai zuwa.

Wannan jeri ya na kunshe da Sanatoci biyu da kuma gwamna mai-ci wanda su ka fito daga jam’iyyun PDP da kuma APC.

1. Ike Ekweremadu

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, ya sanar da Duniya cewa ba zai sake neman takara a 2023 bayan shekaru fiye da 20 ya na bugawa.

A cewarsa ya samu damar yi wa jama’ansa duk wata hidima a mukaman da ya samu kansa. Ekweremadu ya bayyana wannan ne lokacin da ya cika shekaru 57.

KU KARANTA: Gwamnati ta bankado Gwamna Yari ya rika wawurar miliyoyin kudi

Zaben 2023: Ekweremadu, Goje, da Gwamna Masari za su ajiye kambu

Sanata Ike Ekweremadu ba zai nemi kujera a zaben 2023 ba
Source: UGC

2. Mohammed Danjuma Goje

Sanata Mohammed Danjuma Goje wanda ke wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ya shaidawa mutanensa cewa babu shi babu maganar tazarce a 2023.

A wajen wani taro da aka yi a filin wasa da ke Pantami a jihar Gombe, tsohon gwamna ya ce zai bar wa Matasa takara bayan ya rike kujerar Minista da Majalisa.

3. Aminu Bello Masari

Mai girma Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nuna cewa ya na cikin wadanda ba za a sake ganin sunansu a jeringiyar ‘Yan takarar siyasa daga yanzu ba.

Aminu Masari wanda ya taba rike kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya ya tabbatarwa mutane a Katsina cewa zai ajiye siyasa ganin shekarunsa sun ja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel