Gwamnatin jahar Katsina ta gyara Masallacin juma’a a kan kudi naira miliyan 52.9

Gwamnatin jahar Katsina ta gyara Masallacin juma’a a kan kudi naira miliyan 52.9

Gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kashe akalla naira miliyan 52,901,098.74 wajen gyaran babban masallacin juma’a na Usman Danfodio dake unguwar Modoji a cikin garin Katsina.

Jaridar Katsina Post ta ruwaito Gwamna Masari ne ya bayyana haka da kansa yayin da yake gabatar da jawabi gaban majalisar dokokin jahar a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Laraba.

KU KARANTA: Janar Buratai ya gyara firamarin da ya yi a Kaduna, ya bata kyautan littafai 1000

A cewar gwamnan: “An samu cigaba a ayyukan ginin tituna da gadoji da gwamnati ta sanya a gaba a shekarar 2019, inda a yanzu haka an kammala wasu ayyukan ma gaba daya, yayin da wasu kuma na kan hanyar karashewa.

“A shekarar 2019 gwamnati ta bayar da kwangilar titin Gurbin Bature-shimfida-Batsari daya kai tsawon kilomita 48.6 a kan kudi N6,123,676,133.04, sai dai ba’a fara aikin ba sakamakon matsalar tsaro a yankin.

“Haka zalika gwamnatin ta bayar da kwangilar gyaran masallacin Usman Danfodio a kan kudi naira miliyan 52.9, sa’annan ta bayar da kwangilar gyaran ofishin jahar Katsina dake Legas a kan kudi naira miliyan 324.” Inji shi.

A wani labari kuma, babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya gudanar da gyara a tsohuwar makarantar firamarin da ya yi, LEA Unguwar Sarki Kaduna, sa’annan ya baiwa makarantar kyautan littafan karatu guda 1,000.

Buratai ya gudanar da wannan aiki ne ta karkashin gidauniyarsa, watau Tukur and Tukur foundation inda yace a shekarar 1967 ya fara makarantar LEA Unguwar Sarki, kuma ya ga amfanin ilimin daya samu, don haka ya kashe mata makudan kudade.

Ita dai wannan makaranta an samar da ita ne a shekarar 1953 kafin samun yanci, amma a sanadiyyar wannan aikin alheri da Buratai ya gudanar a cikinta, a yanzu tana da; dakin kwamfuta, dakin karatu, ban daki na zamani guda 16, wajen wasan yara da kuma kayan karatu da koyarwa haka zalika ya kara musu azuzuwa 8.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel