Ministan Buhari Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu da Kuri'un da APC Za Ta Samu

Ministan Buhari Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu da Kuri'un da APC Za Ta Samu

  • Solomon Dalung ya ce Bola Ahmed Tinubu zai sha kaye mai tsanani a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa
  • Tsohon minista yana ganin jam’iyyar APC ta rasa goyon bayan Arewa, yankin da ya taimaka mata cin zabe a 2023
  • Ya kara da cewa tsananin yunwa da tsare-tsaren gwamnatin nan sun sa 'yan Najeriya za su bi bayan jam'iyyun hamayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Plateau - Solomon Dalung wanda ya taba zama a Majalisar zartarwa ta kasa ya ce za a lallasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Tsohon ministan wasanni da harkokin matasan Najeriyan yana ganin za a doke APC saboda ta rasa goyon bayan mutanen Arewa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu yana kamfe a jihar Legas a 2023 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Solomon Dalung ya ga Bola Tinubu ya fadi

A hirarsa da tashar Channels, Solomon Dalung ya ce kuri’u miliyan 3.7 kadai suka rage wa Tinubu cikin wadanda ya samu a baya.

Kara karanta wannan

2027: Sabon rikici ya barke tsakanin Wike da gwamnonin APC

Dalilinsa kuwa shi ne yanzu shugaba Muhammadu Buhari ya rasu kuma shi ne ya taimaka wa APC ta lashe zaben shugaban kasa.

Baya ga rashin Buhari, Solomon Dalung ya ce mutanen yankin Arewa su ne suka fi kowa shan wahalar manufofin gwamatin Tinubu.

Dalung wanda yanzu ya sauya sheka zuwa ADC ya ce wahalar da talakawa ke sha da kokarin gwamnatin APC za su yi tasiri a 2027.

Tsohon ministan ya zargi gwamnati mai-ci da kama-karya da ganganci wajen mulki, ya ce wannan ya kara wa jam'iyyun adawa farin-jini.

A ra’ayinsa, Mai girma Tinubu yana cikin shugabannin da gwamnatinsa ta barar da farin jininta wajen talakawa a gaba daya tarihin kasar.

Kuri'un Tinubu sun ragu da miliyan 5.5

Premium Times ta rahoto shi yana cewa cikin kuri’u miliyan 8.7 da Tinubu ya samu a wancan zaben, yanzu ya rasa miliyan 5.5 na Arewa.

Yake cewa dama adadin ya fito ne daga Arewacin kasar saboda tikitin APC na Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

"Abin da zai sa Tinubu ya tumurmusa yan Adawa, ya lashe zaben shugaban ƙasa a 2027"

Mista Dalung ya ce kiyayyar da ake yi wa shugaban kasa ta wuce siyasa, yake cewa fushin talakawan zai yi tasiri a zaben na badi.

Za a maimaita irin zaben Osun a 2027

Shi ma ya kafa hujja da zaben gwamnan jihar Osun, ya ce amfani da kudi ko jam’iyya mai mulki bai tabbatar da samun nasarar zabe a yau.

Duk da gwamnoni, ministoci da manyan APC da suka yi wa jam’iyyar kamfe a zaben Osun, tsohon ministan ya ce ba su iya kai labari ba.

Yanzu yana goyon bayan Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi, ya ce ‘dan takaran na ADC ne ya gaji kuri’un marigayi shugaba Buhari a 2025.

‘Dan adawar ya ce Atiku kwararren ‘dan siyasa ne da ya fahimci Najeriya kuma ya san tsarin tun da ya yi mataimakin shugaban kasa a baya.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Solomon Dalung Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Malamai 600 suke goyon bayan Bola Tinubu

An ji labari malaman jami'o'i sama da 600 daga Arewa sun yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 bayan sun yin bincike.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa Arewa ba za ta juyawa Tinubu baya ba a 2027

Shugaban Jami'ar KASU, Farfesa Abdullahi Musa, ya ce sun ɗauki matakin ne saboda ci gaban da aka samu a fannin ilimi da abubuwan more rayuwa.

Farfesan ya kawo misali da tallafin fiye da ₦1bn da ɗaliban jami’arsa suka samu ta hanyar tsarin NELFUND tare da gudunmawa daga TETFund.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng