Katsina: ‘Yan Sanda sun kashe Nayabale, sun cafke wani Mai satar mutane

Katsina: ‘Yan Sanda sun kashe Nayabale, sun cafke wani Mai satar mutane

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina sun kashe fitinannen Mai garkuwa da mutanen nan watau Abubakar Nayabale, sannan kuma sun kama wani, Tanimu Salisu.

Jami’an tsaron sun kashe Abubakar Nayabale ne a karamar hukumar Kurfi. Kakakin ‘Yan Sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan dazu.

Gambo Isah ya bada wannan sanarwa ne a Ranar Alhamis, 20 ga Watan Junairu, 2020. Jawabin ya ce sun kashe Nayabale ne bayan ya kai hari a wani Kauye.

“A Ranar 17 ga Watan Fubrairun 2020, da kimanin karfe 3:00 na rana, ‘Yan bindiga su takwas a kan babur, dauke da bindigogin AK-47 su ka kai hari a Kumare.”

“A nan su ka shiga buda wuta ta ko ina, kuma su ka sace wani Mutumi mai shekaru 55 mai suna Yahaya Tella.” Kauyen Kumare ya na cikin karamar hukumar Kurfi.

KU KARANTA: An kama wasu buhunan shinkafa boye a cikin murhun gas

Katsina: ‘Yan Sanda sun kashe Nayabale, sun cafke wani Mai satar mutane
Masu satar mutane da dabbobi sun fitini jihar Katsina
Asali: UGC

“Dakarun Operation Puff Adder, a karkashin jagorancin jami’in DPO na karamar hukumar Kurfi, tare da ‘Yan banga su ka yi wuf su ka kai wa ‘Yan bindigan hari.”

“Bayan ba-ta-kashi da bindigogi, an yi dace an kashe Abubakar Nayabale, wanda gawurtaccen Mai satar mutane ne. Sannan kuma an kama wani Tanimu Salisu.”

“Shi Tanimu Salisu mutumin Garin Zakka ne a cikin karamar hukumar Safana a jihar Katsina. An kuma samu babura biyu daga hannun ‘Yan bindigan" Inji DSP Isa.

Kakakin ‘Yan Sandan jihar ya bayyana cewa wani ‘Dan-banga guda ya mutu a sakamakon harin. Amma an yi nasarar ceto wannan mutumin da aka nemi a sace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng