Tun ba a Je Ko'ina ba Shirin Hada kan 'Yan Adawa don Tunkarar Tinubu Ya Gamiu da Cikas

Tun ba a Je Ko'ina ba Shirin Hada kan 'Yan Adawa don Tunkarar Tinubu Ya Gamiu da Cikas

  • Omoyele Sowore ya yi magana kan shi ko jam’iyyar AAC na cikin tattaunawar haɗa ’yan takarar shugaban ƙasa domin samar da ɗan takara guda na adawa
  • Sowore ya ce AAC ba za ta shiga kawance da ‘yan siyasar da ta shafe shekaru tana adawa da tsarin su ba
  • Ya ce jam’iyyarsa na son kawo sauyi daga tsohon tsarin siyasa tare da mai da hankali kan adalci, daidaito da shugabanci nagari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi magana kan sabon shirin hada kan 'yan adawa.

Sowore ya musanta wani rahoton da ya alakanta shi da shirin haɗa wasu ’yan takarar shugaban ƙasa domin samar da ɗan takara guda na adawa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi maganar sayen hannun jari a matatar Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara

Sowore ya yi magana kan zaben 2027
Omoyele Sowore da ke neman shugabancin Najeriya a 2027 Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026.

Ya ce shi da AAC ba sa cikin tattaunawar, kuma ba za su shiga wani kawance irin wannan ba.

Sowore ya ce AAC ba za ta shiga kawance ba

Sowore, wanda a halin yanzu yake hutawa a Amurka gabanin fara kamfen ɗin zaɓe, ya ce shi da jam’iyyarsa ba za su iya shiga kawance da mutanen da suka shafe shekaru suna adawa da su ba.

Ya ce adawar AAC ba ta takaita ga Shugaba Bola Tinubu ko jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kaɗai ba.

A cewarsa, jam’iyyar na adawa ne da tsarin siyasa da hanyoyin gudanar da mulki wadanda a ganinsa, suka haifar da shekaru masu yawa na talauci, cin hanci da rashawa, rashin daidaito, rashin tsaro da koma bayan ci gaba.

Kara karanta wannan

Ko da tsiya tsiya: ADC ta bayyana shirinta kan zaben 2027

Ya bayyana matsayar jam’iyyarsa

Sowore ya ce ya karanta wani rahoto da ke cewa wani kwamitin siyasa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Pat Utomi na shirin tattaunawa da wasu ’yan takarar shugaban ƙasa.

Ya ce an haɗa sunansa cikin mutanen da ake son tattaunawa da su domin samar da ɗan takarar adawa guda a zaɓen 2027.

“Ba za mu shiga tsohon tsarin siyasa ba”

Sowore ya ce matsayar AAC a kan batun ta kasance a bayyane kuma bisa ƙa’ida. Ya bayyana cewa jam’iyyar na da wata manufa ta siyasa da akida wadda ta bambanta, yana mai cewa shirinta na kawo sauyi ya dogara ne kan tsayayyen matsayi na akida, ba neman damar siyasa ko rabon mukamai ba.

Hakazalika ya ce ba za su shiga kawance da tsarin siyasar da suka daɗe suna adawa da shi ba.

Sowore ya ƙara da cewa wasu ’yan siyasar da yanzu suke gabatar da kansu a matsayin “madadin” shugabanci sun taɓa aiki a cikin tsarin siyasar APC, PDP, Labour Party da wasu jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya kawo sabon tsarin tallafi da zai taimaki 'yan Najeriya

Sowore ya barranta da 'yan siyasa
Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Alkawarin Sowore ga ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa Omoyele Sowore, ya yi alkawarin samar da mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.

Sowore, wanda ɗan gwagwarmaya ne, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin AAC za ta samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng