Arewa ya fi ko ina masifar talauci da jahilici a Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Arewa ya fi ko ina masifar talauci da jahilici a Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Arewacin Najeriya ne inda ya fi ko ina talauci. Gwamnatin kasar ta yi wannan bayani ne a jiya Ranar Asabar, 20 ga Watan Fubrairu.

Kamar yadda mu ka samu labari, Ministar kasuwanci da hada-da-hada da zuba hannun jari a Najeriya, Mariam Yalwaji Katagum, ce ta yi wannan jawabi a jihar Katsina.

Karamar Ministar ta bayyana cewa bayan masifar talauci, Arewacin Najeriya ne kan gaba a matsalar jahilci a duk Najeriya. Alkaluman kasar ne su ka tabbatar da wannan.

Ministar ta ce su na kokarin kawo tsare-tsare da za su taimakawa wadannan Yankuna wajen rage talauci da wasu matsalolin zamani da su ka taru su ka yi masu daurin-goro

Ambasada Mariam Yalwaji Katagum ta ce za a iya rage talaucin da ya dabaibaye Arewacin Najeriya ne ta hanyar gina abubuwan more rayuwa ga al’ummar da ke Yankin.

Mariam Yalwaji Katagum duk ta bayyana wannan ne a lokacin da ta kaddamar da wani ginin ofishin ma’aikatarta da hukumar ITF ta yi a Garin Katsina a jiya Ranar Asabar.

Arewa ya fi ko ina masifar talauci da jahilici a Najeriya - Gwamnatin Tarayya
Mariam Katagum ta ce talauci da jahilci sun fi kamari a Arewa
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun yi mummunan ta'adi a jihar Adamawa

“Za ku tuna a jawabin da shugaban kasa Buhari ya yi a Ranar bikin 12 ga Watan Yuni a 2019, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na fitar da mutane miliyan 100 daga talauci.”

Ta ce: “Kamar yadda ya yi alkawari, Buhari ya fara kawo tsare-tsaren da su ka shafi Talakawa kai-tsaye a kasar nan, sannan kuma za su kawo karshen matsalolin Najeriya.”

Mariam Katagum ta ce wadannan tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta kawo za su taimaki musamman Arewacin Najeriya inda yara miliyan 13-14 ba su zuwa makaranta.

A cewar Ministar: “Kuma Yankin (Arewa) ya sha gaban ko ina wajen talauci da jahilci. A game da wannan zan yaba da kokarin da ITF ta ke yi na taimakawa ‘Yan Najeriya.”

Mai martaba Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya saba kokawa a game da irin talaucin da ake fama da shi Arewacin Najeriya, ya na kiran shugabanni su farga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel