Fulani Makiyaya
Gwamnatin jihar Ogun ta fito karara ta gwale zuwan Sunday Igboho jihar domin ya kori Fulani a fadin jihar. Sunday ya ci alwashin korar Fulani a yankin Yarbawa.
Makiyaya da aka kora daga jihar Ondo sun koma Jjihar Ekiti. Manoma sun bayyana cewa da zuwansu har sun shiga gona mai darajar N10m sun lalata komai dake ciki.
Bayan kona gidansa da safiyar yau, Dan gwagwarmayar yarbawa Sunday Igboho ya bayyana cewa, asarar da aka masa sakamakon kona gidansa ya haura Naira miliyan 50.
Sarakunan Fulani sun roki a yafe masu bayan Makiyaya sun tatsi N50m daga satar mutane da saura aika-aikar Miyagun Makiyayan kamar fyade da lalata da matansu.
Kungiyar Fulani ta ce Muhammadu Buhari bai yi masu komai ba, su ka ce abin da ya kamata Gwamnatin Tarayya za ta yi masu idan ta na son su shi ne wurin kiwo.
Wasu sarakunan gargajiya a jihar Ondo sun bayyana cewa korar Fulani a jihar Ondo ba daidai bane. Sun ce kamar kowa Fulani suna da 'yan zama a ko'ina a kasar.
Gwamnan Oyo ya fito ya soki matakin Takwaransa na haramtawa Makiyaya kiwo. Seyi Makinde ya ce ba daidai ba ne a ba Makiyaya Fulani wa’adi su bar kasar da su ke.
Kungiyar dattawan arewa sunyi Allah-wadai da kudurin gwamnan jihar Ondo na fatattakar Fulani a dukkan dazukan dakekewaye da jihar. Sunce hakan ya saba doka.
Gwamnatin jihar Ondo a martaninta na maganar gwamnatin tarayya cewa ba ta yadda a fidda makiyaya daga jihar ba, tana zargin Garba Shehu da goyon bayan barna.
Fulani Makiyaya
Samu kari