Rikicin Makiyaya: Wasu Fulani sun roki al’ummar Garin Iganda su yafe masu

Rikicin Makiyaya: Wasu Fulani sun roki al’ummar Garin Iganda su yafe masu

- Wasu Shugabannin Fulani sun fito sun ba mutanen garin Igangan hakuri

- Manyan kabilar Fulani sun bada hakuri ne a wani taro da aka yi da jama’a

- Sarkin Fulanin kasar Igbo Ora da na Eruwa sun nemi afuwa a taron jiyan

A dalilin aika-aikan da makiyaya su ke yi, wasu shugabannin kabilar Fulani sun roki mutanen garin Iganga, da ke jihar Oyo, su yafe masu.

Jaridar PM News ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi, 24 ga watan Junairu, 2021.

Sarkin Fulanin kasar Igbo Ora, Alhaji Idris Abubakar da takwaransa Sarkin Fulanin kasar Eruwa, Alhaji Sule Mohammed, sun nemi afuwa a madadin makiyaya.

Wadannan jagorori na Fulani sun fito sun nemi yafiyar wadanda aka yi wa laifi da ba dai-dai ba, bayan bayanai sun fito a kan irin barnar da makiyaya suka yi.

KU KARANTA: Babu abin da Gwamatin Buhari ta tsinana mana – Miyetti Allah

Ana zargin makiyaya da yin garkuwa da mutane har suka karbi fansar kimanin Naira miliyan 50, bayan haka miyagun sunyi lalata da yara da matan mutane.

Shugabannin Fulani sun bada hakuri ne a wajen wani taro da aka yi da mazauna garin Iganga domin kawo karshen halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Sauran sarakunan gargajiya sun samu zuwa wajen wannan taro, amma Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Saliu Abdukadir, bai iya halartar zaman da aka yi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa sabuwar Kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Oyo, Ngozi Onadeko da tawagar gwamna a karkashin Fatai Owoseni ta halarci zaman.

Rikicin Makiyaya: Wasu Fulani sun roki al’ummar Garin Iganda su yafe masu
Fulani sun bada hakuri a madadin Makiyaya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Saraki ya yi kira a zauna a kan rikicin Fulani da mutanen Oyo da Ondo

CP Owoseni mai ritaya shi ne mai ba gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shawara a kan harkokin tsaro.

Shugaban kungiyar mutanen Igangan, Lawal Akeem, ya ce sun gaji da abubuwan da ke faruwa, ya kuma zargi Sarkin Fulani da daure wa miyagu gindi.

Dazu kun ji cewa Mai Garin da aka sace a Jihar Katsina ya na tsare a wani kurgurmin daji a Zamfara.

Alhaji Kabir Umar Radda ya yi waya da mutanen gidansa bayan an yi garkuwa da shi, kuma ya shaida wa ‘Yanuwansa cewa ya na wani jeji a jihar Zamfara.

Alhaji Radda ya ce ‘yan bindigan da su ka sace shi a ranar Juma'a, ba su yi masa komai ba, kuma kawo yanzu ba su bukaci a biya wasu kudin fansa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel