Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo

Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo

- Wasu sarakunan gargajiya a jihar Ondo sun yi Allah wadai da umarnin korar Fulani a jihar

- Sun bayyana cewa, Fulani kamar kowane kabila suna da hakkin zama a duk inda suke so

- Sun kuma yi kira ga gwamnatin da ta daidaita al'amarin yadda zai taimakawa tsaron jihar

Sarakunan gargajiya a jihar Ondo a ranar Alhamis sun bayyana cewa Fulani kamar kowane kabila suna da 'yanci su zauna tare da gudanar da ayyukansu na halal a koina a cikin kasar nan ciki har da jihar Ondo, The Nation ta ruwaito.

Sarakunan gargajiyan da suka bayyana goyon baya kan umarnin da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya bayar kan makiyaya su fice daga dazukun gwamnati a cikin kwanaki bakwai ya ce dole ne Fulani su mutunta haƙƙin dukiyar mutane.

Da yake karanta sanarwar da aka fitar bayan taron gaggawa na sarakunan, Oba Kadiri Momoh, Olukare na Ikare, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya nuna wa duniya cewa shi uba ne ga kowa ba tare da la’akari da bambancin kabila ba.

KU KARANTA: Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar

Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo
Fulani na da 'yancin zama a Ondo, in ji sarakunan gargajiya a Ondo Hoto: Blog Master Media
Asali: UGC

Ya kuma bukaci Buhari da ya gargadi mataimakansa ga nuna sakaci kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro a kasar.

Sanarwar ta bukaci Gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma, kwamitin kudu maso yamma a majalisar kasa da kuma majalisun dokokin jihohi da su yi amfani da hanyoyin da tsarin mulki ya ba su wajen shawo kan masu aikata miyagun laifuffuka.

Ta yi Allah wadai da abin da ta kira wani yunkuri na ganganci da wasu mutane ke yi don karkatar da umarnin da Gwamnan ya bayar game da dazukan gwamnati cewa an nemi Fulani su bar jiharmu.

A cewar sanarwar, “Abin lura ne cewa hatta 'yan asalin jihar Ondo ba su da ikon amfani da gandun daji ba tare da izini ba.”

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya tace ta shiryawa 'yan N-Power goma na arziki

A wani labarin, Kungiyar dattawan Arewa a ranar Laraba ta bayyana matsayin ta kan umarnin da aka ba wa Fulani makiyaya su bar dazukan Ondo da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, Aminiya ta ruwaito.

Kungiyar ta kara da cewa abun mamaki ne matuka jin irin wannan umarnin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel