Ka tura sojoji don kare 'yan Arewa a yankin kudu maso yamma, Unongo ya fadawa Buhari
- Wani babba a kungiyar dattawan arewa ya kalubalanci shugaba Buhari kan gyara arewa
- Dattijon ya kira yi shugaban da mayar da hankali kan yankinsa na arewa duba da yadda yankin yake
- Ya kuma bukaci shugaban da ya gaggauta tura sojoji domin su kare 'yan arewa dake yankin kuduncin Najeriya
Ministan ci gaban karafa a jamhuriya ta biyu kuma wanda ya hada taron kungiyar dattawan Arewa (NEF), Paul Unongo, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ba da umarnin tura sojoji don kare 'yan arewa da ke zaune a Kudu maso Kudu da sauran sassan kasar.
Dattijon, wanda ya yi magana a wata hira da Sunday Tribune, ya kuma bukaci Buhari da ya yi amfani da shugabancinsa don mayar da hankali kan Arewa, yana mai cewa "idan Arewa ba ta samu ci gaba ba, sauran kasar ba za ta ji dadi ba."
“Shi ne shugaban kasa. Shi dan Arewa ne. Ya san abubuwan da yankin yake so. Idan Arewa ba ta yi kyau ba, sauran kasar ba zai yi kyau ba. Amma idan Arewa ta samu ci gaba, babu wani mutum ko wata kungiya da za ta tashi ta kalubalanci kasar ko wani bangare na kasar.
KU KARANTA: Kudin Intanet: Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta kasuwancin Bitcoin
“Arewa ta mallaki kashi 70 na dukkan filayen kasar nan. Muna da ƙwarewar gudanarwa kuma muna da iko. Mun kawo shi mulki. Bai kamata yaji tsoron bunkasa yankin sa ba.
“Ba mu ce bai kamata ya bunkasa sauran sassan kasar ba, amma yankin Arewa da ke baya a kusan kowane bangare dole ne ya ja hankalinsa.
"Babban abin da zai sa a gaba yanzu ya kamata ya zama Arewa. Kamata ya yi ya yi amfani da karfin da yake da shi yanzu ya hada kan mutanen yankin,” inji shi.
KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata
A wani labarin, Wani shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce masu neman kafa kasar Biafra da Oduduwa ba su da bambanci da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.
Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Asabar yayin da yake sharhi kan halin rashin tsaro a kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng