Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya

Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya

- Kungiyar gwamnonin yankin arewa ta bukaci a daina kai wa Fulani makiyaya hari a kudancin kasar nan

- Ta yi wannan kiran ne bayan kamarin rigingimu, kashe makiyaya da barnatar da dukiyoyinsu da ake yi

- Gwamnonin sun tabbatar da cewa akwai marasa laifi a cikin Fulanin kuma a mika masu laifi ga hukumomi

Kungiyar gwamnonin arewa (NEF) ta yi kira a kan a daina harar Fulani makiyaya da ke kudu maso gabas, kudu maso yamma da kuma kudu-kudu a kasar nan.

Gwamnonin sun ce akwai bukatar a kiyayi makiyaya da babu ruwansu sannan a mika masu laifi hannun hukumomin tsaro.

Amma gwamnonin kudu maso yamma sun yi martani ga wannan kiran inda suka ce akwai bukatar hukumomi a arewacin Najeriya su dakatar da makasan makiyaya da ke zabga barna a kudu.

KU KARANTA: Jami'an tsaro da farin kaya sun cafke Nastura da wasu jiga-jigan CNG a Kaduna

Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya
Gwamnonin arewa sun yi magana da kakkausar murya a kan harin da ake kaiwa makiyaya. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa jihohi masu yawa da ke kudu sun fara rikici tsakanin mazaunansu da makiyaya wanda hakan ya kawo mace-mace da barnar dukiyoyi.

A yayin da jama'a a kudanci ke zargin makiyaya da barna tare da ta'addanci, wasu shugabannin Fulani da ke zama a yankunan sun ce ba kowa bane mai laifi a cikinsu.

KU KARANTA: Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi

A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya kushe korar da ake wa 'yan kasar nan daga wasu sassan Najeriya inda yace dan Najeriya yana da damar zabar inda yake son zama.

Tsokacinsa na zuwa ne bayan kiran da ake ta yi ga Fulani makiyaya da su bar wasu sassan kasar nan a kan rashin tsaro.

Farko daga cikin wannna bukatar ta fito ne daga gwamnatin jihar Ondo a kan cewa makiyaya su bar dajikan jihar, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel