Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun

Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun

- Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana cewa ita bata gayyaci Sunday Igboho ba zuwa jihar

- Sunday Igboho ya furucin cewa an gayyaci shi jihar don yaki da fulani makiyaya a jihar

- Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa jihar gidan kowa ne 'yan Najeriya da baki masu shigowa

Gwamnatin Ogun a ranar Litinin ta karyata rahotannin da ke nuna cewa ta nemi taimakon Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho, don magance laifuka a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Abdulwaheed Odusile, ya yi watsi da rahoton a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta sa’o’i bayan Igboho ya isa jihar.

Mista Odusile ya ce rahoton wanda ya samo asali ne daga wata hira da Remmy Hazzan, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga Gwamna Dapo Abiodun, aka nakalto ba daga garesu take ba.

KU KARANTA: Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata

Gwamnatin Ogun ta gwale zuwan Sunday Igboho don yaki da Fulani
Gwamnatin Ogun ta gwale zuwan Sunday Igboho don yaki da Fulani Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

“An karkata akalar tattaunawar ne don a samu sakamako mai kayatarwa.

“A cikin tattaunawar, Hazzan ya ce gwamnatin jihar, a tsarin da ta saba na gudanar da mulki, za ta ci gaba da aiki da duk masu ruwa da tsaki, ciki da wajen jihar don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Abin takaici, duk da haka, wadannan kalaman an juya su ne da gangan wanda ke nuna cewa jihar ta gayyaci Mr. (Igboho) don taimakawa wajen magance rashin tsaro."

“Wannan abin takaici ne kuma yaudara ce kawai.

“Gwamnatin Dapo Abiodun ta jagoranci, tun daga farkonta, an san ta da kowa da kowa a cikin hanyoyinta na mulkinta, hada kai da kuma yin hulda da dimbin masu ruwa da tsaki ciki har da batun tsaro.

“Wannan ya haifar da cimma nasarar da muke da shi a matsayinmu na mafi tsaro a kasar nan."

Mista Odusile ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da jan hankali tare da maraba da duk wadanda ke da kyawawan dalilai na zama da kuma yin aiki a jihar, ya kara da cewa "Ogun gida ce ga dukkan 'yan Najeriya da kuma baki."

KU KARANTA: Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong

Ya kuma jaddada cewa, jihar ba za ta aminta da duk wata kungiya ko wasu mutane da ke kokarin lalata zaman lafiya, tsaro da zamantakewar 'yan kasa ba.

A wani labarin, Wani mai yakin kwatar 'yancin Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa jihar Ogun yana cewa ya kai ziyarar ne don ya fatattaki makiyaya.

Dama Igboho ya bayyana a labarai yana bai wa makiyayan da suke wuraren Ibarapa dake jihar Oyo wa'adin kwanakin da za su kwashe ya nasu ya nasu su bar garin. Bayan nan ne aka kai wa gidan sarkin fulanin yankin farmaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel