Wata Cuta Ta Rage Mugun Iri, Ta Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga da Ya Addabi Jama'a

Wata Cuta Ta Rage Mugun Iri, Ta Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga da Ya Addabi Jama'a

  • Rahotanni sun sun nuna cewa cutar kwalara ta barke a sansanin miyagu kuma ta kashe akalla 'yan bindiga shida a jihar Zamfara
  • Daga cikin wadanda suka mutu akwai Abubakar Dattiya, mataimakin kasurgumin dan bindiga, Muhammadu Gwaska
  • An ce barkewar cutar ta faru ne a maboyar 'yan bindigar da ke karamar hukumar Anka, sai dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Rahotanni sun bayyana cewa barkewar cutar kwalara ta yi sanadin mutuwar akalla wasu da ake zargin 'yan bindiga ne su shida a jihar Zamfara.

Daga cikin wadanda cutar ta zama ajalinsu har da mataimakin wani fitaccen shugaban 'yan bindiga, Muhammadu Gwaska.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro da na al'umma sun ce barkewar cutar ta faru ne a maboyar Muhammadu Gwaska da ke karamar hukumar Anka, inda cutar ta bazu cikin gaggawa tare da kashe mutane da dama cikin 'yan kwanaki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nuna rashin imani kan mata da jarirai a wani kazamin hari a Katsina

Mataimakin Gwaska ya rasa ransa

Daya daga cikin wadanda rahotanni suka ce sun mutu shi ne Abubakar Dattiya, wanda ake bayyana a matsayin mataimakin jagoran dabar yan bindiga, Muhammadu Gwaska.

Majiyoyi sun ce mutuwarsa na iya yin tasiri ga jagoranci da kuma ayyukan kungiyar 'yan bindigar, wadand suka addabi al'umma a yankin Anka da kewaye.

Cutar ta bazu cikin sauri a Zamfara

A cewar majiyoyin da suka san abin da ya faru, wasu daga cikin 'yan kungiyar sun fara nuna alamomin cutar kwalara kafin daga bisani cutar ta bazu a cikin maboyar yan bindigar.

Rahoton ya ce saboda rashin samun kulawar lafiya cikin sauki a maboyar da ke cikin daji, cutar ta yi sanadin mutuwar mutane da dama cikin kankanin lokaci.

Jami'an tsaro na tattara bayanai

Har zuwa yanzu hukumomi tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Sai dai majiyoyin tsaro sun ce jami'an leken asiri na ci gaba da sa ido domin tantance hakikanin adadin wadanda suka mutu da kuma irin tasirin da hakan zai yi ga karfin kungiyar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

Rahoton ya zo ne yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kai farmaki kan maboyar 'yan bindiga a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Dakarun yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki a jihar Zamfara Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Wasu mazauna yankunan da abin ya shafa sun bayyana farin cikinsu, tare da fatan cewa lamarin zai rage karfin kungiyar wajen kai hare-hare kan fararen hula.

Sai dai shugabannin al'umma sun bukaci jami'an tsaro da su ci gaba da matsa lamba kan 'yan bindiga domin rusa sauran maboyarsu da dawo da zaman lafiya a yankin.

Jami'an tsaro sun daƙile hari a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Zamfara tare da sojoji da masu sa-kai sun dakile harin ‘yan bindiga a hanyar Gidan Giye zuwa Magazu da ke ƙaramar hukumar Tsafe.

Jami'an tsaron sun samu wannan nasara ne bayan samun sshihan bayanan sirri cewa yan bindigar na kokarin tsallake titin domin kai hari kan al'umma.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar yayin artabun, yayin da wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262