Makiyaya 4,000 sun yi hijra daga jihohin kudu zuwa jihar Kaduna
- Wasu makiyaya da suka tsere daga harin mutanen yankin kudu sun fara dawowa jihohin arewa
- Kimanin makiyaya 4,000 ne suka tattara nasu-ya-nasu suka dawo wani yankin jihar Kaduna
- Sun bayyana cewa da yawansu sun rasa komai, suna kuma bukatar abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum
Sakamakon umarnin fatattakar makiyaya masu aikata laifuka a wasu jihohin kudu, kimanin makiyaya 4,000 sun bar jihohin kudu zuwa Kaduna, Nigerian Tribune ta ruwaito.
An tattaro cewa makiyayan tun makon da ya gabata suna dawowa zuwa garin Labduga, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.
Wani jami’in Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Hussaini Abdullahi ya ce, “Ya zuwa yanzu mun tabbatar da dawowar kimanin dubu hudu, kuma har yanzu wasu suna nan tafe.”
Ya ce hukumarsa da wata kungiya mai zaman kanta, mai suna 'Early Recovery Initiative' suna gudanar da binciken kwakwaf ga makiyayan da suka tsere don neman taimako.
KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma
“Ba mu tanadar musu da wani sansani na musamman ba, suna zama ne cikin al'ummar da ta saukesu, suna samun taimakon gaggawa daga dangi da kuma wasu mutane na gari.
“Mafi yawansu sun rasa abinda suke samu na rayuwa, sun gaya mana cewa suna bukatar abinci da abubuwan da ba abinci ba cikin gaggawa, amma kuma mun lura cewa suna fama da matsalar halayyar dan adam kuma a saboda haka, suna bukatar shawarwari.
"Nan ba da dadewa ba za mu ziyarce su kuma mu gudanar da bincike kan halin da suke ciki don ganin inda za mu taimaka musu."
Shima da yake magana, Daraktan Yada Labarai, reshen jihar Kaduna na kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), Ibrahim Bayero ya bayyana cewa hakika halin da suke ciki abin tausayi ne.
“Mun fara tattara mambobin mu don ganin yadda za mu taimaka musu. Kamar yadda muke tsammanin karin su, ” inji shi.
KU KARANTA: IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU
A wani labarin, Shugaban majalisar dattijai, Yahaya Abdullahi, ya ce zauren dattijai zai tattauna kan matsalar rikicin makiyaya Fulani a duk fadin kasar a ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.
Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa, ya ce mataimakinsa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng