Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnonin arewa sun soki kiwo a fili

Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnonin arewa sun soki kiwo a fili

- Kungiyar gwamnonin arewa sun nuna rashin dacewar ci gaba da kiwo a budadden wuri

- Kungiyar ta fidda sanarwar kiwon a budadden wuri wani tsohon abune da ya kamata a daina

- Kungiyar ta yi alkawarin wayar da kan makiyaya don shigar da su tsarin kiwo na zamani

Gwamnoni a Arewa a ranar Talata sun bayyana batun kiwo a fili da makiyaya suke yi a matsayin tsohon abu. Ya kamata ya kare, The Nation ta ruwaito.

Wannan shawarar ita ce sakamakon, taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar.

Shawarar ta yi daidai da ra'ayin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya ce ya kamata makiyaya su rungumi kiwo a waje daya su daina kiwon shanun su daga Arewa zuwa Kudu shi ne zaman lafiya.

KU KARANTA: Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnonin arewa sun soki kiwo a budadden wuri
Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnonin arewa sun soki kiwo a budadden wuri Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Majalisar Dattawa ta yi gargadin cewa idan aka bar rikicin manoma da makiyaya ya yi zafi, zai iya haifar da yakin kabilanci da addini da kuma yunwa.

Gwamnonin Arewa, a cewar sanarwar taron da shugabanta, Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya fitar, sun yanke shawarar wayar da kan makiyaya kan bukatar yin kiwon ta hanyoyin zamani da za a amince da su.

Sun ce tsarin kiwo na yanzu da ake gudanarwa musamman ta hanyar kiwo a bayyane ba zai iya dorewa ba saboda yawan birane da yawan jama'ar kasar.

"Sakamakon haka, Kungiyar ta yanke shawarar fadakar da makiyaya da karfi."

Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafawa Jihohi da tallafi kai tsaye don aiwatar da ayyukan samar da tsarin kiwon zamani wanda zai zama abin da za su zama hujja na karya adawa ga cikakken aiwatar da sabbin hanyoyin kiwon dabbobi.

Sun kuma yanke shawarar shigar da dattawa da matasa cikin tattaunawa mai karfi da nufin wanzar da zaman lafiya da tsaro a arewa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

A wani labarin, GYB2PYB Youth Support Group ta yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa matakan da suka dauka har zuwa yanzu don sanya APC a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, Vanguard News ta ruwaito.

A jiya gwamnan jihar Kogi tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Buni na jihar Yobe sun karbi tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel