"An Yi Kuskure": Babban Fasto Ya Fadi Makomar Obi da Kwankwaso a Zaben 2027

"An Yi Kuskure": Babban Fasto Ya Fadi Makomar Obi da Kwankwaso a Zaben 2027

  • Fitaccen fasto a Najeriya, Primate Ayodele ya ce waiwayi yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa, Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Faston wanda ke ikirarin zai sanar da yan takarar da za su lashe zabe mai zuwa ya bayyana kuskuren da NDC ta yi wajen tsayar da 'yan takara
  • Sabon hasashensa na zuwa ne bayan ya ce an yi masa gurguwar fahimta game da makomar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana hangaensa game da nasarar yan takarar jam'iyyar NDC.

Ya bayyana cewa ba ya ganin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, za su kai ga nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba.

Kara karanta wannan

Babban malamin addini ya yi gyara kan batun Tinubu zai fadi zabe

An hango kalubalen NDC a babban zaben 2027
Yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso Hoto; Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Tribune Online ta kawo labarin cewa Ayodele ya bayyana haka ne yayin da yake wa'azi ga mabiyansa har ya tabo maganar zaben 2027 mai zuwa.

An yi hasashe kan Obi da Kwankwaso

Daily Post ta wallafa cewa Primate Ayodele ya ce jam'iyyar NDC ta yi babban kuskure da ta zabi shiga zabe ita kadai maimakon hade kai da jam'iyyar ADC domin kafa kawancen siyasa.

A watan Mayun bana ne Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka fice daga ADC zuwa NDC, inda suka danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma shari'o'in da ke addabar tsohuwar jam'iyyarsu.

Fasto ya ce hadewa da ADC zai fi wa NDC alheri
Babban fasto a Najeriya, Primate Ayodele Hoto; Primate Elijah Ayodele
Source: Facebook

Sai dai Ayodele ya ce wannan mataki bai taimaka wa NDC ba, yana mai cewa da sun hade da ADC ne da sun fi samun karfi a siyasa.

Ya ce:

"Ku dubi jam'iyyar NDC a Najeriya. Da ace za ku saurara, maimakon ku tsaya ku kadai, da kun hade da ADC domin kafa kawance."

Kara karanta wannan

Komai ya fito fili, INEC ta saki bayanan karatun Tinubu da Shettima

An hangowa NDC rashin nasara

Malamin ya ci gaba da cewa bai ga NDC tana cikin manyan jam'iyyun da za su taka muhimmiyar rawa a zaben shugaban kasa mai zuwa ba.

A cewarsa:

"Kun tsaya ku kadai, amma NDC ba ta cikin lissafi. Suna cewa komai yana lafiya, amma ni ban ga komai yana tafiya yadda suke zato ba. Ban ga bi da Kwankwaso za su kai ko'ina a zaben shugaban kasa na 2027 ba."

Ayodele ya jaddada cewa matakin da NDC ta dauka na tsayawa ita kadai ya raunana damar jam'iyyar gabanin babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kotu ta yi watsi da karar NDC

A wani labarin, mun wallafa cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar hamayya ta NDC mai adawa a Najeriya ta shigar a gabanta game da dokar zaben Najeriya.

Kotun ta ce Sashe na 138 na Dokar Zabe ya dace da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, domin yana bayyana hanya da wa’adin shigar da korafi a kan abubuwan da suka shafi zabe a kasar.

Mai shari’a Muhammed Umar ya ce dole ne a kalubalanci cancantar dan takara tun a matakin kafin zabe, kuma hakan ko kadan bai saba da dokar kasa ko cin karo da dokar zaben Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng