Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa

Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa

- Gamayyar Kungiyoyin Arewa sun yarda da shawarar Sheikh Gumi kan dokar kiwo

- Kungiyoyin sun ce da bukatar a kebe filayen kiwo don magance rikicin makiyaya

- Sun kuma ce za su shige gaba don tunkarar Gwamnati ta bada filayen kiwo ga fulani

Gamayyar Kungiyoyin Arewa a ranar Litinin ta mara wa wani fitaccen malamin addinin Islama, Sheik Ahmad Gumi baya, wanda a makon da ya gabata ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da kasafin kudin tsaro wajen magance bukatun ’yan fashi da makiyaya.

Kakakin gamayyar, Abdul-azeez Suleiman, wanda ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch, ya gabatar da wasu shawarwari wadanda suka karfafa matsayin malamin na Islama.

Ku tuna cewa Gumi, a yayin ziyarar sa zuwa dazukan Tubali da Makkai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, ya yi kira ga 'yan fashi da su rungumi zaman lafiya.

KU KARANTA: Nasarorin da na cimma sun kai a rubuta littatafai akai, in ji Burutai

Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa
Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake bai gwamnati shawara kan amfani da kasafin kudin tsaro don biyan bukatun ‘yan fashi.

“Irin wadannan biliyoyi (na Naira) za su isa fiye da yadda za a yi amfani da hankali wajen magance duk bukatun Fulani da ke dauke da makamai, gami da samar musu da ababen more rayuwa, basu horo da kuma basu jari da ake bukata.”

Suleiman ya ce, “A bisa ƙa’ida, babu wani damuwa kan shawarwarin Sheikh Gumi idan muna da gwamnati mai sauraro da kuma manazarta masu son cimma gaskiya.

"A namu bangaren, za mu wuce gaba kan shawarwarin Sheikh Gumi don neman gwamnati ta bada filayen da suka dace a duk fadin kasar tare da kirkirar wuraren kiwo da hanyoyin shanu.

"Muna kuma ba da shawara ga shelar Manufofin Kasa kan Kiwo da Bunkasa Kiwo domin biyan bukatun dukkan al'ummomin makiyaya a duk inda suke a cikin kasar."

KU KARANTA: Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

A wani labarin, Wani shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce masu neman kafa kasar Biafra da Oduduwa ba su da bambanci da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.

Gumi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Pidgin a ranar Asabar yayin da yake sharhi kan halin rashin tsaro a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.