Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho

Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho

- A safiyar yau Talata ne a ka cinna ma gidan wani dan gwagwamaryar yarbawa wuta

- Dan gwagwamaryar ya bayyana cewa an kona masa kadarorin da suka haura N50m

- Ya kuma bayyana cewa akwai hannun yarbawan yankin a yayin kona gidan nasa

Bayarben dan gwagwarmaya, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce abin da aka lalata a tsohon gidansa da masu kone-kone suka kona kalla ya haura Naira miliyan 50, The Punch ta ruwaito.

Da yake bayyana abin da ya fahimta game da harin da aka kai wa tsohon gidansa, Igboho wanda ya zanta da manema labarai ya ce masu kone-konen suna harbe-harbe kafin su shiga.

Ya ce, “da misalin karfe 3:30 na safiyar yau, kannena da ke zaune a tsohon gidana sun garzaya zuwa kofar gidana don su tashe ni, suna cewa wasu 'yan fashi sun zo gidan, suna harbe-harbe, suka fasa kofa, suka cinna wa gidan wuta.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta sanar da bude kofar shiga makarantar sojoji NDA

Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho
Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho Hoto: Legit.ng
Source: UGC

"Mutanen biyu da ke gidan sun yi nasarar tserewa. A lokacin da na isa wurin, 'yan fashin sun tsere. Don haka, mun kira jami’an kashe gobara don taimaka mana wajen kashe wutar. ”

Da aka tambaye shi ko wa yake zargi da kai harin, sai ya ce, "A yanzu, bana zargin kowa."

Ya bayyana imanin cewa tabbas wadanda suka kai hari gidansa tabbas sun samu taimako daga wasu Yarabawa.

“Abin da na ga abin mamaki shi ne yadda wasu Yarabawa ke goyon bayan makiyaya don cinna wa gidana wuta. Ina bakin ciki da hakan,” in ji shi.

Dangane da irin barnar da aka yi wa gidansa, ya ce, "Darajan abin da aka lalata a gidana ba zai iya kasa da Naira miliyan 50 ba."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan…

A wani labarin, Hukumar yan sandan jihar Oyo ta ce ta samu labarin cewa wasu yan bindiga cike da motar bas da tasi sun banka wuta gidan mutumin da ya ke kokarin korar Fulani daga kasar Yarbawa, Sunday Igboho.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata, Punch ta ruwaito.

Fadeyi ya ce an bayyanawa yan sanda cewa sai da yan bindigan suka yi harbe-harbe sama kafin suka bankawa gidan wuta dake unguwar Soka, Ibadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel