Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata

Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata

- Zauren majalisar dattawa ta bayyana cewa a gobe Talata za ta zauna kan lamarin Fulani

- Majalisar dattawan zai tattauana ne kan mafita da ya kamata a samu kan Fulani makiyaya

- Hakazalika majiya ta ruwaito a baya fadar shugaban kasa ta barranta da umarnin korar Fulani a Ondo

Shugaban majalisar dattijai, Yahaya Abdullahi, ya ce zauren dattijai zai tattauna kan matsalar rikicin makiyaya Fulani a duk fadin kasar a ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.

Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa, ya ce mataimakinsa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.

Abdullahi ya ce Gwamnatin Tarayya na da rawar da za ta taka wajen magance rikicin, yana mai jaddada cewa ya kamata a karfafa shugabannin siyasa na cikin gida don samar da mafita mai dorewa.

KU KARANTA: Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata
Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Fadar Shugaban kasa ta yi Allah-wadai da umarnin da Gwamnatin Jihar Ondo ta bayar kwanan nan cewa Fulani makiyaya su bar gandun dajin na Ondo.

Amma Abdullahi ya ce maimakon ta tsunduma kanta cikin batun, ya kamata fadar Shugaban kasa ta karfafa wa shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya gwiwa don taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar.

Ya ce, “Wannan wani irin rikici ne wanda ke fuskantar yanayin tafiyar da mulki inda wasu 'yan siyasa da ’yan kasuwar kabilanci ke shigowa cikin harkar da lalata lamarin.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ba lallai idanunta su kai kan kowane bangare da ake rikici a kasar ta kuma kai dauki ba.

“Wannan shi ne abin da gwamnoni a matakan su ya kamata su dinga yi ba wai su dinga dangata abin zuwa ga shugaban kasa a koda yaushe ba, don magance wata takaddama a nan da can Makamai nawa Gwamnatin Tarayya ke da su?

KU KARANTA: Nasarorin da na cimma sun kai a rubuta littatafai akai, in ji Burutai

A wani labarin, Shahararren mai rajin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya bayyana cewa yana da cikakken shiri da ya kamata don yaki da Boko Haram ba tare da goyon bayan gwamnati ba.

Igboho ya yi wannan bayanin ne a wata hira ta bidiyo da aka fitar a shekarar 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel