Uba Sani Ya Cika Alkawari ga Iyalan Ummulkhairi da na Faston da Ya Mutu a Hannun 'Yan Bindiga
- Gwamna Uba Sani ya sake jaddada cewa gwamnatin Kaduna za ta ci gaba da tallafa wa wadanda rikici ya shafa
- Gwamnatin jihar ta samar wa iyalan marigayi Ven. Edwin Achi da Ummulkhair Aliyu gidaje tare da daukar nauyin karatun ‘ya’yansu
- Uba Sani ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da gidaje, ilimi, kiwon lafiya da tallafin tattalin arziki ga wadanda rikici ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa wadanda rikici ya shafa a fadin jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar wa iyalan da abin ya shafa gidaje, ilimi, kiwon lafiya da kuma hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu.

Source: Facebook
Uba Sani ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Gwamna ya yanke hukunci, ya yi wa shugaba Tinubu alkawarin 95% na kuri'u a zaben 2027
Ya bayyana hakan ne bayan ya karbi bazawarar marigayi Ven. Edwin Achi, Misis Sarah Achi, da mijin marigayiya Ummulkhair Aliyu, Malam Usman Aliyu.
Iyalai sun gode wa Uba Sani
Misis Sarah Achi ta ziyarci gwamnan tare da Archbishop na Kaduna Diocese, Most Rev. Timothy Yahaya. Shi kuma Malam Usman Aliyu ya je tare da Sheikh Haliru Maraya.
A cewar gwamnan, iyalan biyu sun kai masa ziyarar ne domin nuna godiya kan tallafin da gwamnatin jihar Kaduna ta ba su bayan rasuwar ‘yan uwansu.
“Na yi farin cikin karbar Misis Sarah Achi, matar marigayi Ven. Edwin Achi, wacce ta kawo mini ziyarar girmamawa domin bayyana godiyarta daga zuciya. Archbishop na Kaduna Diocese, Most Rev. Timothy Yahaya, ya raka ta.
“Na kuma karbi Malam Usman Aliyu, mijin marigayiya Ummulkhair Aliyu, wacce rayuwarta ta kare cikin wani lamari mai ban tausayi na kisan gilla da jama’a suka yi a Maraban Jos. Sheikh Haliru Maraya ya raka shi.”
- Gwamna Uba Sani
Tallafin da gwamnati ta bayar
Gwamna Uba Sani ya tuna cewa bayan faruwar al’amuran biyu, ya ziyarci iyalan da kansa domin yi musu ta’aziyya.
Ya ce ya tabbatar musu cewa gwamnatinsa za ta tsaya tare da su ba kawai ta hanyar nuna alhini ba.
“Domin cika wannan alkawari, mun samar wa kowanne daga cikin iyalan gida, mun ba su tallafin kudi domin taimaka musu su sake gina rayuwarsu, sannan muka dauki nauyin karatun ‘ya’yansu.”
- Gwamna Uba Sani
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar wa wadanda rikici ya shafa fata, mutunci da damar inganta rayuwa.
A cewarsa, za a cimma hakan ne ta hanyar samar musu da ingantattun gidaje, ilimi mai kyau, kiwon lafiya da kuma tallafin tattalin arziki mai dorewa.

Source: Facebook
Uba Sani ya raba gidaje 100
Gwamnan ya ce wannan manufa ce ta sa gwamnatin jihar ta raba gidaje 100 ga wadanda ‘yan bindiga suka shafa a fadin jihar Kaduna.
Uba Sani ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce manufar ita ce a gina jihar Kaduna mai aminci, zaman lafiya da kuma bai wa kowane dan kasa damar shiga cikin al’amuran jihar.
Uba Sani ya zabi mataimaki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya zabi abokin takara don zaben 2027.
Sanata Uba Sani, ya sanar da shugaban hukumar KADIRS), Jerry Adams, a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

