Kungiyar dattawan arewa ta yi Allah-wadai da kudurin korar Fulani

Kungiyar dattawan arewa ta yi Allah-wadai da kudurin korar Fulani

- Kungiyar dattawan arewa sun bukaci gwamnan jihar Ondo ya janye maganarsa na korar Fulani

- Sun bayyana cewa hakan ya saba dokar Najeriya na hakkin zama a duk inda mutum ya zaba

- Sun kuma bukaci ya bincika abubuwan da ke faruwa don kawo gyara a harkar tsaron jihar

Kungiyar dattawan Arewa a ranar Laraba ta bayyana matsayin ta kan umarnin da aka ba wa Fulani makiyaya su bar dazukan Ondo da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, Aminiya ta ruwaito.

Kungiyar ta kara da cewa abun mamaki ne matuka jin irin wannan umarnin.

Kungiyar, wanda ta gargadi gwamnan da kada ya bari masu yin barna su haifar da kalubalen tsaro a kasar da umarnin sa, ta bukace shi "da ya soke umarnin sa kan Fulani, ko kuma ya bayyana matsayin sa idan har ba a fahimce shi ba."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gwamnati ta yadda a bude makarantu

Kungiyar dattawan arewa ta yi Allah-wadai da kudurin korar Fulani
Kungiyar dattawan arewa ta yi Allah-wadai da kudurin korar Fulani Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da yada labarai, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, dandalin ya yi ikirarin cewa Akeredolu a matsayin babban lauya ya kamata ya san cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba shi ikon haka ba

Sun bayyana cewa duk wani dan Najeriya yana da damar zama a inda yake so idan baya karya doka yayin aiwatarwa.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Ondo ya umarci Fulani makiyaya da ke zaune a dazuzzuka daban-daban na jihar da su kaura domin dakile matsalar masu satar mutane a jihar.

Amma NEF ta ce idan har akwai masu laifi a tsakanin Fulani makiyaya da ke zaune a Jihar, ya kamata Gwamnan ya bi matakan da suka dace don gano su da kuma magance su.

Kungiyar ta ci gaba da cewa yana da matukar hadari kuma ba za a yarda da nunawa Fulani zagon kasa ba tare da bi da su a wajen dokokin kasa kamar sauran 'yan Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya tallafawa yara 10m da ba sa makaranta

A wani labarin, Gwamnatin jihar Ondo, a ranar Laraba, ta dage kan cewa dole ne makiyaya su bi umarnin kwanaki bakwai da Gwamna Rotimi Akeredolu ya ba su na barin gandun dajin da ke jihar.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Donald Ojogo, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da shirin Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels Television wanda The PUNCH ke lura da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel