Shettima Ya Yi Magana yayin da Jama'a suka Sako Tinubu a Gaba da Suka
- Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta cancanci yabo kan sauye-sauyen da ta aiwatar a fannoni daban-daban
- Shettima ya danganta hauhawar ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje daga dala biliyan 3 zuwa kusan dala biliyan 52 da manufofin gwamnatin Tinubu
- Ya kuma yabawa gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, bisa goyon bayan da ya bai wa sauye-sauyen gwamnatin tarayya tun daga shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta – Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cancanci yabo maimakon suka saboda sauye-sauyen tattalin arziki da ta aiwatar.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron tattalin arziki da zuba jari na jihar Delta da aka gudanar a Asaba, inda ya yabawa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo.

Source: Facebook
Channels TV ta rahoto cewa taron ya samu halartar shugabannin siyasa, 'yan kasuwa da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar.
Shettima ya fadi nasarorin Tinubu
A cewar mataimakin shugaban ƙasar, Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannin tattalin arziki sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.
Ya ce:
"Farfesa Soludo, ka yi wa gwamnatin tarayya babban aiki musamman wajen sanar da 'yan Najeriya halin da muka fito."
Ya ƙara da cewa:
"Mun taso daga lokacin da ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta kai dala biliyan 3, lokacin da ake fama da ƙarancin kuɗi da ficewar masu zuba jari.
'Yanzu muna samun karuwar shigowar masu zuba jari, kuma kudin ajiyarmu ta haura dala biliyan 52 a cikin duniyar yau mai cike da ƙalubale. Ina ganin shugaban ƙasa ya cancanci yabo ba suka ba."
An yaba wa Gwamna Soludo
Shettima ya kuma yabawa gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, saboda yadda ya mara wa manufofin gwamnatin tarayya baya tun lokacin zaɓen shekarar 2023.
Ya ce yawaitar shirya tarukan zuba jari da jihohi ke yi alama ce ta kyakkyawar gasa da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihohi.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ware dala miliyan 100 domin rage haɗarin zuba jari a jihar.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta tanadi fiye da hekta 12,000 na filayen noma domin masu zuba jari, tare da jaddada cewa Delta na da gabar teku da za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ruwa.
Ga sashen bayanin da Shettima ya yi a bidiyon da hadiminsa ya wallafa a X:
Katsina za ta raba Naira biliyan 4
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Katsina ta kammala shirye-shiryen raba Naira biliyan 4 ga mazabu 361 domin gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.
An bayyana cewa kowace mazaba za ta karɓi Naira miliyan 10 bayan amincewar gwamna Dikko Umaru Radda domin aiwatar da ayyukan da mazauna yankin suka fifita.
Gwamnatin ta kuma gargadi shugabannin al'umma da su tabbatar an yi amfani da kudin yadda ya kamata, tana mai cewa duk wanda aka samu ya karkatar da su zai fuskanci hukunci.
Asali: Legit.ng

