An Samu Matsala a Kotu kan Sharudan Belin Shugaban Miyetti Allah, Bodejo
- Wata kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi sauraron buƙatar shugaban Miyetti Allah, Bello Bodejo wanda ake tuhuma
- Mai shari'a Inyang Ekwo ya bayyana cewa hutun kotu na gabatowa, don haka ba za a kammala sauraron ƙarar ba
- EFCC na tuhumar Bello Bodejo da karɓar dala miliyan 2.63 ta hannu ba tare da bin doka ba, kan zargin karya dokokin hana safarar kuɗaɗe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi sauraron sabon buƙatar shugaban Miyetti Allah na ƙasa, Alhaji Bello Bodejo.
Bodeji na neman a sauya sharudan belin da kotun ta ba shi bayan tuhumarsa da ake yi kan hannu a ta'addanci.

Source: Facebook
Mai shari'a Inyang Ekwo ya ba Bodejo beli a ranar 20 ga Yuli kan kuɗin N2bn tare da mutane biyu da za su tsaya masa, kowannensu da irin wannan ƙima, cewar The Nation.
Bodejo: Umarnin da kotu ta bayar
Kotun ta umarci cewa ɗaya daga cikin masu tsaya masa ya gabatar da shaidar biyan haraji na shekaru uku kuma ya kasance mazaunin yankin ikon kotun.
An kuma umarci cewa mai tsaya masa na biyu ya mallaki fili a Abuja da darajarsa ta kai Naira biliyan biyu kafin a amince da belin.
Lokacin da aka ambaci shari'ar a ranar Alhamis, lauyan Bodejo, M. E. Sheriff, ya sanar da kotun cewa sun shigar da buƙatar sauya wasu daga cikin sharudan belin.
Lauyan EFCC mai gabatar da ƙara, Fatai Erewunmi, ya ce an ba su kwafin buƙatar kuma sun mayar da martani ta hanyar gabatar da takardar ƙin amincewa.
Mai shari'a Ekwo ya ce ganin yadda ake takaddama kan buƙatar da kuma hutun kotu da ke tafe, ba zai yiwu a kammala sauraronta ba.
Saboda haka ya shawarci ɓangarorin su garzaya wajen alkalin hutun kotu domin a saurari buƙatar, sannan a dawo kotunsa domin ci gaba da shari'ar.

Kara karanta wannan
Ganduje ya tsokano NDC da Obidents, sun yi masa raddi mai zafi kan taba Obi, Kwankwaso
Kotun ta ɗage ci gaba da shari'ar zuwa ranar 5 ga Oktoba domin fara sauraron shaidu kan tuhume-tuhumen da EFCC ta gabatar.
EFCC na zargin Bello Bodejo da laifin wanke kuɗaɗe, tana cewa ya karɓi dala miliyan 2.63 ta hannu daga tsohon Akanta Janar na Bauchi, Sa'idu Abubakar.
A cewar hukumar, kuɗaɗen sun zarce iyakar kuɗin da doka ta amince a karɓa ta hannu ba tare da bi ta banki ba, lamarin da ya sa aka gurfanar da shi.
Tuhume-tuhumen guda shida sun haɗa da karɓar dala $100,000, $200,000, $100,000, $980,000, $750,000 da kuma $500,000 a lokuta daban-daban tsakanin shekarar 2022 da 2024.
EFCC ta ce waɗannan kuɗaɗe an karɓe su ba tare da bin tanadin dokokin hana safarar kuɗaɗe na shekarun 2011 da 2022 ba, saboda ba a bi ta cibiyar kuɗi ba.
Gwamna ya magantu kan kisan Miyetti Allah
An ji cewa gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da kisan shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku da dan uwansa.
Alia ya ce kisan ya faru ne a lokacin da zaman lafiya ke kara dawowa a sassan Benue, yana mai cewa hakan barazana ce ga kokarin sulhu.
Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, su kamo masu hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su.
Asali: Legit.ng
