Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo

Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo

- Biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar Ondo ta yi fatattakan dukkan makiyaya, gwamnatin tarayya ta gargadi gwamnan jihar

- Kwamishinan labarai na jihar Ondo ya yi martanin cewa Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi

- Kwamishinan ya bayyana cewa babu hannun Shugaba Buhari cikin maganar Garba Shehu

Gwamnatin jihar Ondo, a ranar Laraba, ta dage kan cewa dole ne makiyaya su bi umarnin kwanaki bakwai da Gwamna Rotimi Akeredolu ya ba su na barin gandun dajin da ke jihar.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Donald Ojogo, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da shirin Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels Television wanda The PUNCH ke lura da shi.

Ojogo ya mayar da martani ne ga wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

KU KARANTA: Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu

Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo
Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Kwamishinan ya ce Shugaban kasa bai goyi bayan kalaman na fadar shugaban kasa ba, ya kara da cewa dole ne Shehu ya yi bayanin dalilin da ya sa ya goyi bayan masu aikata laifuka wadanda ke buya da sunan makiyaya.

Ya ce, “Wani abu ne tabbatacce, Shugaba Muhammadu Buhari duba da yadda ya gabata, da yanayin kishin kasa da kuma yiwa kasa hidima da aka san shi da shi, mai yiwuwa ba shi ne ya gabatar da wannan maganar ba.

"Kusan na shawo kan tunanin cewa Garba Shehu bai fitar da wannan maganar ba saboda hakan na iya zama mai matukar hadari ga hadin kan kasar nan.

"Ina jira in tabbatar idan gaskiya ne, to, watakila ya yi kuskuren magana ga mutanen Najeriya.”

Ojogo ya ce idan har aka tabbatar da cewa Shehu ya yi wannan magana, to, “yana nufin wasu mutane a fadar shugaban kasa, wasu jami’ai a fadar shugaban kasar suna kokarin haifar da matsala ga Shugaba Muhammadu Buhari

"Dole ne mu yaba da kokarin wannan shugaban kasa a yakin da yake yi da rashin tsaro a fadin kasar nan. Rashin tsaro ya zama batun ƙasar; babu wani sashe na kasar da ya tsira daga rikici ”.

Shehu ya kare hakkin makiyaya na zama a ko ina a cikin kasar, yana mai cewa gwamnan ba zai iya "ta fatattakar dubban makiyayan wadanda suka rayu duk tsawon rayuwarsu a cikin jihar ba sakamakon shigowar dazuzzuka da masu aikata laifi suka yi".

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wani dan damfara mai ikirarin shi jami'in EFCC ne a Abuja

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya sake jaddada bukatar kasashen makwabta su kasance masu kiyaye muradun juna a koda yaushe, yana mai cewa dorewar juna ya dogara da juna, Vanugard News ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kasar Benin, Patrice Talon, wanda ya kai ziyarar gani da ido a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.